Otedola Ya Goyi bayan Dangote a Rikicinsa da 'yan Kasuwar Mai, Ya Shawarci DAPPMAN

Otedola Ya Goyi bayan Dangote a Rikicinsa da 'yan Kasuwar Mai, Ya Shawarci DAPPMAN

  • Femi Otedola, fitaccen dan kasuwa a Najeriya ya bayyana matatar Dangote a matsayin mafita daga matsalolin mai a Najeriya
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke sukar yadda 'yan kasuwar man fetur karkashin kungiyar DAPPMAN ke kokarin takure Dangote
  • Otedole ya bai wa kungiyar sirrin ci gaba da fafatawa a kasuwar mai idan suna ganin za su iya bugawa da matatar Dangote a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Hamshakin ɗan kasuwa kuma shugaban kamfanin Geregu Power Plc, Femi Otedola, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Aliko Dangote.

Wannan ya biyo bayan rikicin da ke tsakanin Matatar Dangote da kungiyar DAPPMAN, masu rumbunan ajiya da dillalan kayayyakin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta dakatar da hulda da wasu yan kasuwa a Najeriya, ta fadi dalilai

Otedola ya goyi bayan Dangote
Hoton Alhaji Aliko Dangote, Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Hoto: Getty
Source: Getty Images

PremiumTimes ta ruwaito cewa a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Otedola ya taya Dangote murna kan nasarar kafa matatar mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana ta a matsayin babbar nasara ga ‘yancin Najeriya a fannin makamashi da makomar tattalin arziki.

Otedola ya mara wa Dangote baya

The Guardian ta wallafa cewa Otedola ya kuma yaba da matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya kawo sabuwar damar samun sauki.

Otedola, wanda shi ne ya kafa DAPPMAN a 2002, ya soki kungiyar bisa rashin sabunta tsarin kasuwancinta, yana cewa lokaci ya wuce na dogaro da tallafin mai don shigo da kaya.

Ya bayyana cewa a baya, kafa rumbunan ajiya na man fetur na da amfani saboda tsarin shigo da mai ya kasance mara inganci.

Otedola ya ce DAPPMAN ta sake fasalin kasuwanci
Hoton Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote Hoto: Getty
Source: Getty Images

Amma a cewarsa tun da yanzu Najeriya na da matatar mai mai aiki da kyau, kamar ta Dangote, tsarin na baya ya zama tsohon tarihi.

Kara karanta wannan

ADC ta fadi gwamnan da doka ta yarje wa Tinubu ya sauke daga kujerarsa

Ya ce:

“Na ba wasu daga cikin 'yan DAPPMAN shawara a bara da su sayar da rumbunansu, domin yanzu yawancinsu ba su da amfani.”

Dangote: Otedola ya shawarci DAPPMAN

A cewarsa, DAPPMAN tana neman Dangote ya biya N1.5trn don raba mansa ga kwastomomi, amma ya ce hakan ba zai yiwu ba.

Ya jaddada cewa lokaci ya yi da kungiyar ta koma mayar da hankali kan tashoshin saida mai kai tsaye, ba wai rumbunan da ba sa aiki ba.

A cewar Otedole:

“Matatar Dangote ba matsala ba ce, ita ce mafita."

Ya bukaci su zuba jari a sababbin hanyoyi ko su haɗa kai su sayi matatar Fatakwai idan suna da kwarin gwiwar za su iya fafatawa a kasuwar mai.

Matatar Dangote ta dakatar da wasu 'yan kasuwa

A wani labarin, mun wallafa cewa Matatar Dangote ta amince da dakatar da siyar da kaya ga wasu daga cikin ‘yan kasuwa a Najeriya tun daga ranar 18 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

Matatar ta bayyana cewa an dauki matakin ne saboda rashin bin sababbin tsarin aiki daga kamfanin, saboda haka ake ganin ci gaba da mu'amalarsu ba shi da amfani.

A cikin wata wasika, kamfanin ya bayyana cewa matakin “gyara ne” da aka ɗauka don tabbatar da cewa rarraba man fetur ya zama mai sauƙi, inganci, da gaskiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng