Jonathan Ya Kada Hantar Shugabanni, Ya Fadi Abin da Kamata a Yi Wa Marasa Katabus
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana kan barazanar da tsarin dimokuradiyya ke fuskanta a nahiyar Afrika
- Jonathan ya bayyana cewa wasu shugabanni na amfani magudin zabe wajen ci gaba da zama a kan madafun iko
- Tsohon shugaban kaaan ya nuna cewa ya kamata a rika gudanar da sahihin zabe ta yadda za a kori shugabannin da ba su tabuka komai ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Ghana - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi magana kan dimokuradiyya da shugabanni a nahiyar Afrika.
Goodluck Jonathan ya ce duk wani shugaba da ya gaza yin katabus, ya kamata a kawar da shi idan aka gudanar da sahihin zaɓe.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Jonathan ya yi wannan jawabi ne a taron shekarar 2025 na gidauniyar Goodluck Jonathan Foundation (GJF) da aka gudanar a Accra, Ghana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin tsohon shugaban kasan na cikin wata sanarwa da jami’in sadarwa na gidauniyar GHF, Mr. Wealth Dickson Ominabo, ya fitar a ranar Asabar, 20 ga watan Satumban 2025, rahoton jaridar PM News ya tabbatar da labarin.
Goodluck Jonathan ya koka kan magudin zabe
Goodluck Jonathan ya bayyana maguɗin zaɓe a matsayin ɗaya daga cikin manyan barazanar dimokuraɗiyya a Afirka.
Ya ce muddin masu ruwa da tsaki ba su haɗa kai domin sake tunani da gyara tsarin dimokuradiyya ba, akwai yiwuwar ta rushe a nahiyar.
Tsohon shugaban kasan ya ce idan dimokuraɗiyya ta kasa cika burin jama’a, hakan na iya buɗe kofa ga mulkin kama-karya.
Ya kara da cewa dole ne shugabanni su jajirce wajen aiwatar da irin dimokuraɗiyyar da za ta tabbatar da kyakkyawar makoma ga manyan gobe, inda muryarsu za ta kasance da muhimmanci.
Wace shawara Jonathan ya bada kan shugabanni?
"Dimokuraɗiyya a nahiyar Afirka tana fuskantar rauni da barazanar rushewa, sai dai idan masu ruwa da tsaki sun haɗa kai domin sake tunani da gyara ta."
"Maguɗin zaɓe na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan barazana a Afirka.”
"Dole ne mu a Afirka mu fara nazarin dimokuraɗiyyar mu, mu sake tunani a kanta ta yadda za ta yi aiki da kyau gare mu da jama’armu."
"Ɗaya daga cikin matsalolin ita ce tsarin zaɓenmu. Mutane na maguɗi a tsarin domin su ci gaba da zama a kan mulki ta kowace hanya.”
"Da muna da sahihin zaɓe, duk wani shugaba da ya gaza yin aiki, za a kore shi ta hanyar kada shi a zaɓe. Amma a lamarinmu, mutane na amfani da tsarin wajen dora kansu a mulki ko da jama’a ba sa so.”
"Mutanenmu suna son su more ‘yancinsu. Suna son kuri’unsu su kirgu a lokacin zaɓe. Suna son wakilcin da ya haɗa kowa. Suna son ingantaccen ilimi. Mutanenmu suna son tsaro. Suna son samun ingantaccen kiwon lafiya."
"Suna son ayyukan yi. Suna son mutunci. Idan shugabanni suka gaza samar da waɗannan muhimman bukatu, jama’a na gaza amincewa da gwamnati.”
- Goodluck Jonathan

Source: Facebook
Wike ya soki masu son Jonathan ya yi takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ragargaji wadanda su ke kokarin jawo Goodluck Jonathan, ya yi takara a zaben 2027.
Ministan ya bayyana cewa masu son Goodluck Jonathan ya yi takara ba komai su ke yi ba face kokarin haddasa rikici.
Nyesom Wike ya nuna takaicinsa ganin waɗanda ke ƙoƙarin jawo Jonathan a yanzu, su ne suka hana shi samun nasarar wa’adi na biyu a 2015.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


