Sarakuna 2 Sun Yi 'Rashin Kunya', An Dakatar da Su daga Sarauta a Najeriya
- Mutum biyu masu rike da sarautar gargajiya sun fusata Sarkin kasar Saki da ke jihar Oyo, Oba Khalid Oyeniyi Olabisi
- Basaraken ya dakatar da sarakunan biyu, Baale Ilua na Sakiland da Kelli-Ile na Sakiland bisa zarginsu da aikata laifuffukan rashin da'a
- Sarkin Saki ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne bayan bin matakan jawo hankali don su gyara halayensu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Sarkin ƙasar Saki a Jihar Oyo, Oba Khalid Oyeniyi Olabisi, ya dakatar da manyan sarakuna biyu har sai baba-ta-gani kan zarge-zargen rashin da'a.
Sarkin wanda ake martabawa a yankin ya da dakatar da sarakunan ne saboda zargin rashin biyayya da kuma shiga harkar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa wadanda lamarin ya shafa su ne Kilani Azeez O. wanda aka dakatar daga matsayin Baale Ilua na Saki, da Timothy Oyesiji daga matsayin Baale Kelli-Ile na Saki.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya
Dalilin dakatar da sarakuna 2 a Oyo
A cikin wata sanarwa da masarautar Saki ta fitar a ranar Laraba, Sarkin ya bayyana cewa:
“Wannan hukunci da majalisar sarakunan Okere ta dauka ya biyo bayan karɓar koke-koke da bincike kan zargin rashin biyayya, shiga harkar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, take doka, da raina kujerar sarautar Okere na Sakiland.
“Bisa ikon da nake da shi a matsayin Okere na Sakiland, ni Oba Dr Sur Khalid Oyeniyi Olabisi Oyedepo III, na dakatar da Cif Kilani Azeez O. daga matsayin Baale Ilua na Saki da Timothy Oyesiji daga matsayin Baale Kelli-Ile na Saki.
"Wannan hukunci zai fara aiki nan take har sai an ji sabon umarni daga gare ni ya biyo baya.
Mai Martaba ya gargadi sauran sarakunan Saki
Sarkin ya kara da cewa ba zai lamunci irin wannan halaye daga kowane dan kasarsa ba, balle kuma wanda aka ba amanar shugabanci na sarautar gargajiya.
"Duk yunƙurin da aka yi na ankarar da su domin su gyara halinsu ya ci tura, sun ci gaba da nuna girman kai, lamarin da ya tilasta daukar wannan matakin domin dawo da su kan hanya.
“Ina gargadin sauran shugabannin gargajiya da kada su shiga irin waɗannan munanan ayyuka, ciki har da harkar da ba ta dace ba ko kuma zaluntar jama’a.
"Za a ci gaba da sa ido sosai a kan ayyukansu, kuma duk wanda ya sake kaucewa doka zai fuskanci hukunci mai tsanani."
- Oba Khalid Oyeniyi.

Source: Facebook
Daga karshe, Sarkin Saki ya shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan a hulɗarsu da Cif Kilani Azeez O. da Cif Timothy Oyesiji, domin an cire su daga matsayin Baale Ilua na Saki da Baale Kelli-Ile na Saki, in ji Daily Post.
Za a nada Sarkin Ibadan a jihar Oyo
A wani labarin, kun ji cewa an shirya nadin tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan watau Olubadan ranar 26 ga watan Satumba, 2025.
Bayanai sun nuna cewa za a naɗa tsohon gwamna , Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Tuni dai gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya amince da nadin Oba Rashidi Ladoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan.
Asali: Legit.ng

