Shugaban APC Ya Yabi Manufofin Tinubu, Ya Fadi Canjin da Suka Kawo a Najeriya

Shugaban APC Ya Yabi Manufofin Tinubu, Ya Fadi Canjin da Suka Kawo a Najeriya

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya tabo batun sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu yake aiwatarwa
  • Ya bayyana cewa tuni manufofin su ka fara haifar da sakamako mai kyau a fannin tattalin arzikin kasar nan
  • Shugaban na APC ya nuna cewa jihohi da kananan hukumomi suna ganin amfanin sauye-sauyen da shugaban kasan ya kawo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban na APC ya yaba kan sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar tun bayan hawansa mulki.

Shugaban APC ya yabi Tinubu
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @DOlusegun, @nentaweyilwatda
Source: Twitter

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels Tv.

Shugaban APC ya yabi manufofin Tinubu

Shugaban na APC ya bayyana sauye-sauyen a matsayin masu muhimmanci kuma masu amfani, inda ya jaddada cewa cire tallafin mai ya samu amincewar ‘yan Najeriya baki ɗaya kafin a aiwatar da shi.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 2, Gbajabiamila ya haska wani dalilin Tinubu na cire tallafin fetur

Farfesa Nentawe ya lura cewa tun daga kungiyoyin farar hula har zuwa ‘yan adawar siyasa, sun amince cewa tallafin mai ba zai dawwama ba, kuma dole ne a kawar da shi.

A cewarsa, manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, irin su cire tallafi da sauye-sauye a fannin haraji, sun fara haifar da sakamako mai kyau a faɗin kasar nan.

Nentawe ya ce kudaden shiga sun karu

Shugaban na APC ya bayyana cewa kudaden, shiga da ake samu a kasar nan sun karu sosai.

"Babu wata jiha a yau da ba ta iya biyan albashi. Gwamnonin da ke fama da rashin iya biyan hakkokin ma’aikata yanzu suna biyan su cikin sauki saboda karin kudaden shiga."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Farfesa Nentawe ya kara da cewa manufofin sun karfafa tattalin arziki a matakai uku na gwamnati, lamarin da ya ba su damar mayar da hankali sosai kan ci gaba da kuma bayar da ayyuka ga jama’a.

Manufofin Tinubu sun kawo ci gaba

Shugaban APC ya ce wadannan manufofi, duk da cewa sun kasance masu tsauri a farkon aiwatarwa, suna kafa ginshikin ci gaba mai dorewa da wadata ga ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

Ya jaddada 'yan Najeriya za su ga amfaninsu yayin da ake ci gaba da aiwatar da su.

Nentawe ya yabawa Bola Tinubu
Hoton shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Karanta wasu labaran kan Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu ya yanke hutunsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen hutun da ya tafi yi a kasar Faransa.

Shugaba Bola Tinubu ya yanke hutun ba kamar yadda aka tsara ba tun da farko a lokacin da zai bar Najeriya a ranar, 4 ga watan Satumban 2025.

A cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, Shugaba Tinubu zai dawo ne domin ci gaba da jan ragamar harkokin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng