Ambaliya Ta Mamaye Adamawa, an Gargadi Sokoto da Wasu Jihohi 12
- Ma’aikatar Muhalli ta yi gargadin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi 14 ciki har da Legas da Adamawa daga ranar 16 zuwa 18 ga Satumba
- Hukumar NEMA ta tabbatar da cewa ruwan sama mai tsanani ya riga ya haifar da ambaliya a wasu sassan Yola, inda gidaje da dama suka lalace
- An ce za a iya samun ambaliya a garuruwa 52 da ke cikin jihohin da aka fitar da hasashen, ciki har da yankunan Kogi, Sokoto, Kebbi da Cross River
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sake fitar da sabon hasashen ambaliyar ruwa da ake sa tsammanin za ta shafi jihohi 14 ciki har da Legas, Adamawa da Sokoto.
Hasashen wanda Cibiyar Kula da Ambaliya ta kasa ta wallafa ya nuna cewa ana sa ran ruwan sama mai tsanani daga 16 zuwa 18 ga watan Satumba a jihohi daban-daban da garuruwa 52.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa daraktan Sashen Kula da Ambaliya, Usman Abdullahi Bokani, ne ya sanya hannu kan rahoton da aka fitar ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da ambaliya za ta shafa
Jihohin da ake hasashen ambaliyar sun hada da Akwa Ibom, Anambra, Adamawa, Cross River, Bayelsa, Delta, Kaduna, Kebbi, Katsina, Rivers, Imo, Sokoto, Ondo da kuma Legas.
A cewar rahoton, cikin garuruwan da ake hasashen akwai Uyo a Akwa Ibom, Yenagoa a Bayelsa, Asaba a Delta, Jimeta a Adamawa, Calabar a Cross River, Birnin Kebbi a Kebbi, da Epe a Legas.
Ma’aikatar ta bukaci jama’a musamman mazauna yankunan kogin Benue da Neja su dauki matakan kariya.
Haka zalika ta gargadi mazauna kananan hukumomi da ke bakin kogin Gongola su gaggauta barin gidajensu.
An yi ambaliya a jihar Adamawa
Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar Talata, Adamawa ta fara fuskantar tasirin ambaliyar sakamakon ruwan sama mai tsanani da aka tafka daga Asuba zuwa rana.
Hukumar NEMA ta bayyana cewa ambaliyar ta shafi akalla yankuna 13 a cikin kananan hukumomin Yola ta Arewa da ta Kudu.
Kungiyoyin ceto da suka hada da hukumar kashe gobara, jami’an tsaro da masu aikin sa-kai sun gudanar da aikin ceto da kuma kwashe jama’a zuwa sansanonin wucin gadi.

Source: Original
Matakan ceto jama'a a Adamawa
A cikin sanarwar da NEMA ta wallafa a X, an ce an kwashe mata, yara, tsofaffi da marasa lafiya daga wuraren da suka fi hadari zuwa wuraren da aka tanada na wucin gadi.
Hukumar ta kara da cewa an gudanar da bincike na gaggawa domin tantance barnar da ambaliyar ta yi ga gidaje, hanyoyi da sauran muhimman abubuwa.
An yi wannan aikin ne tare da hadin gwiwar hukumar kula da jin kai ta jihar Adamawa, hukumomin tsaro, da sauran kungiyoyin agaji.
Legit ta tattauna da Aliyu Idris
Wani dan jihar Adamawa da ambaliyar ta shafa, Aliyu Idris Ali ya zantawa Legit Hausa cewa mutane da dama suna cikin damuwa.
Ya ce:
"Gaskiya ambaliyar ta shafi mutane. Ruwan ya zo da safe, karfe 6:00 kafin mutane su shirya. Mutane ko karya wa ba su yi ba.
"Ambaliyar ta shiga kasuwanni da dama saboda haka ba a samu damar da za a saye kayan abinci da sauransu ba."
Ambaliya ta yi barna a Zariya
A wani rahoton, kun ji cewa ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a garin Zariya na jihar Kaduna.
Wani rahoto ya nuna cewa ruwan da ya shafe lokaci yana sauka ya tafi da mutanen da suke cikin harkokinsu.
Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin mutanen da ruwan ya tafi da su sun mutu, ciki har da 'yan makaranta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


