Yadda aka Gano Gawar Ƴar Shekara 4 da Ruwa Ya Tafi da Ita a Kaduna

Yadda aka Gano Gawar Ƴar Shekara 4 da Ruwa Ya Tafi da Ita a Kaduna

  • An gano gawar wata yarinya ‘yar shekara 3hudu da ruwan ambaliya ya yi awon gaba da ita a Kaduna
  • Mamakon ruwan ya tafi da yarinyar mai suna Hanifa tare da ƴan uwansa, kuma ita ce ta karshen gano wa
  • An gano Hanifa kwanaki shida bayan afkuwar mummunan lamarin da ya kiɗima jama'a da ƴar uwanta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – A ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025 ne aka gano gawar Haneefa, yarinya ‘yar shekara hudu da ruwa ta tafi da ita a Tudun Jukun, Zariya, a jihar Kaduna.

Ambaliyar ruwa ta faru ne bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a ranar 8 ga Satumba, 2025 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai biyu.

Kara karanta wannan

'Za a sheƙa ruwa na kwana 5,' An faɗi jihohin Arewa 10 da za su gamu da ambaliya

An gano gawar Haneefa a Zariya
Taswirar jihar Kaduna Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa ɗaliban da su ka rasu sun haɗa da Fatima Sani Danmarke daga makarantar SBRS Funtua da Yusuf Surajo da ake kira Abba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gano gawar Hanifa a Kaduna

Daily Post ta wallafa cewa sanarwar da ƙungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross reshen Zariya ya fitar ta ce, an samo gawar Hanifa.

Jami'in hukumar, Abdulmumin Adamu ya ce:

“Da 11:00 na safe a ranar Lahadi, an gano gawar Haneefa a unguwar Gangaren Kasan Killaco, Gyallesu, Zariya. Wannan ya tabbatar da cewa an gano duk wadanda ambaliyar ta rutsa da shi a wannan lamari.”

Haneefa na goye a bayan ƴar uwarta Fatima suna ƙoƙarin tsallake ruwa, amma igiyar ruwa ta tafi da su tare da sanadiyyar rasa rayukansu.

Ƴan uwan Haneefa sun shiga jimami

Dangin Hanifa sun bayyana halin da suka shiga bayan an kai ga nasarar gano gawarta kwanaki shida da ambaliya.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Gwamnatin Yobe ta tsage gaskiya kan kisan mutum sama da 80

Kakanta, Malam Suleiman daga Layin Adamu Mai Aljana, ya tabbatar da cewa an kawo gawar yarinyar gida a ranar Lahadi bayan gano ta.

An gano Haneefa kwanaki shida bayan ambaliya
Hoton gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Ya ce:

"An kira ni da 12.00 na rana aka sanar da ni cewa an samo gawar Haneefa. Na yi gaggawar zuwa gida don tabbatar da labarin. Sai muka shirya jana’izar da aka gudanar da misalin 1:00 na rana."
"A baya ma mun riga mun yi sallar janaza ta Salatul Ga'ib a masallacin Isa Cikon Kwami bayan sallar magrib.”

Ya yi addu’a ga dukkanin waɗanda suka taimaka wajen gano gawar diyarsu, tare da mika godiya ga al’ummar da suka tausaya da ba su goyon baya a wannan mawuyacin hali.

Legit Hausa ta samu labarin cewa mahaifin yarinyar bayan nan a halin yanzu.

An samu mamakon ruwan a Kaduna

A baya, mun wallafa cewa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya jawo ambaliya mai ƙarfi da ya yi barna a garin Manchok, a masarautar Moro’a, karamar hukumar Kaura ta Kaduna.

Mazauna yankin sun bayyana halin da suke ciki, suna cewa ambaliyar ruwan da aka yi bayan kwanaki uku na mamakon ruwan sama ya jefa su a tsaka mai wuya sosai.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Duniya Awuwu Sambo, daya daga cikin mazaunan Manchok, ya ce kayan gidansa sun lalace sosai, ciki har da kayayyakin wutar lantarki, kujeru da sauran kayan daki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng