Da Gaske Wike Yana Fama da Cutar Ciwon Zuciya? Abin da Muka Sani zuwa Yanzu
- An yi wata wallafa mai cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, na fama da cutar zuciya mai tsanani
- Rahoton ya yi ikirarin cewa yanzu haka Wike yana kwance a wani asibitin kasar waje don duba lafiyarsa
- Hakan na zuwa ne bayan rashin ganin Wike a bainar jama’a ba tun ranar 3 ga watan Satumba, abin da ya kara zuga jita-jitar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - An yada jita-jita a kafafen sada zumunta cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, baya da lafiya.
Jita-jitar ta nuna cewa Wike yana fama da cutar ciwon zuciya kuma yana kwance a asibitin kasar waje.

Source: Twitter
An yada jita-jita kan lafiyar Wike
Mutane sama da mutum 12,000 sun ga rubutun wanda ya ke magana kan rashin lafiyar Wike.
Rubutun na cewa:
"Da dumi-dumi: Wike ya kamu da cutar ciwon zuciya a UK. Yanzu yana fama da rashin lafiya."
Za a iya ganin rubuttukan da ke magana kan rashin lafiyar Wike a nan da nan da nan.
Ya gaskiyar lamarin yake?
Mun gano cewa shafin Sahara Reporters ya buga labari kan rashin lafiyar Wike.
Shafin watsa labaran ya ce majiyoyi da ke da masaniya kan rashin lafiyar Ministan, sun sanar da cewa ya kamu da cutar zuciya kuma yanzu haka yana karbar magana a wani asibiti da ke UK.
Bayan su dai, babu wata sahihiyar jarida da ta wallafa labarin.
Rashin ganin Wike ya jawo tambayoyi
An lura cewa Wike bai bayyana a taron jama’a ba tun ranar 3 ga Satumba, lokacin da ya halarci bikin kaddamar da wani aikin titi a Abuja.
Tun daga lokacin, an ga wasu mutane na wakiltarsa a manyan tarurruka guda biyu.
A ranar 4 ga Satumba, shugaban ma’aikatansa, Chidi Amadi, ya wakilce shi wajen rabon taki mai rahusa ga manoma a Abuja.

Kara karanta wannan
Fitaccen jarumin fim a Najeriya ya saki bidiyo ana tsaka da jita jitar cewa ya mutu
Hakazalika a ranar 11 ga Satumba, karamar ministar Abuja, Mariya Mahmud Bunkure, ta wakilce shi a taron shekara na kungiyar Association of Paediatric Surgeons of Nigeria (APSON)
Wannan rashin fitowarsa ya kara hura wutar jita-jitar cewa yana jinya a wajen kasar.

Source: Twitter
Har yanzu babu martani daga kakakinsa
Kakakin Wike, Lere Olayinka, wanda aka saba ganin yana mayar da martani cikin gaggawa a kafar sada zumunta ta X (Twitter), bai ce uffan kan jita-jitar ba.
A halin yanzu, babu wata hujja daga manyan kafafen yada labarai da ke tabbatar da ikirarin cewa Wike na fama da cutar ciwon zuciya.
An shawarci Wike ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam'iyyar APC, Tonye Cole, ya ba Nyesom Wike, shawara.
Tonye Cole ya shawarci ministan na babban birnin tarayya Abuja kan ya koma jam'iyyar APC, domin kawo karshen rudani kan inda akalar siyasarsa ta nufa.
Tsohon dan takarar gwamnan ya bayyana cewa komawar Wike zuwa APC zai ba sauran jam'iyyun siyasa damar samun ci gaban da su ke so, ba tare da yi musu shishshigi ba.
Asali: Legit.ng
