Bayan Shekara 2, Gbajabiamila Ya Haska Wani Dalilin Tinubu Na Cire Tallafin Man Fetur
- Femi Gbajabiamila ya sake tabo batun cire tallafin man fetur da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasan ya ce cire tallafin mai da Tinubu ya yi alamar jarumta ce ta fuskar shugabanci
- Ya ce gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu tsauri tun daga rana ta farko don ganin cewa kasar nan ta gyaru
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abeokuta, jihar Ogun - Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa kuma, Femi Gbajabiamila, ya yi magana kan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi ba don siyasa ba ne, illa don nuna jarumtar shugabanci.

Source: Facebook
Tsofaffin 'yan majalisa sun yi taro
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Femi Gbajabiamila ya yi wannan jawabi ne a taron tsofaffin 'yan majalisu na Kudancin Najeriya, wanda aka gudanar a birnin Abeokuta, jihar Ogun
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya samu halartar manyan ’yan siyasa ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani, tsofaffin shugabannin majalisar wakilai Yakubu Dogara da Patricia Etteh.
Sauran sun hada da sakataren jam’iyyar APC na kasa Dr. Ajibola Bashiru, gwamnan Ogun Dapo Abiodun, da kakakin majalisar dokokin Ogun, Oludaisi Elemide.
Gbajabiamila ya fadi matakan da Tinubu ya dauka
A cewarsa, cire tallafin mai, gyaran tsarin haraji da kafa hukumar NELFUND da ke bai wa kowanne yaro dan Najeriya damar samun ilimin jami’a, na daga cikin shaidun cewa Tinubu na da hangen nesa na dogon lokaci kan gyaran kasa.
"Gwamnatin tarayya ta daina biyan kudaden tallafi da aka yi wa lakabi da karya, wadanda ’yan tsiraru ne kawai ke cin moriyarsu."
"Kowanne dan Najeriya yanzu yana da tabbacin samun ilimin gaba da sakandare ta hanyar NELFUND. Bisa rattaba hannu kan dokar gyaran haraji, Shugaba Bola Tinubu ya bude sabon zamani na adalcin tattalin arziki wanda ya ginu kan gaskiya, rikon amana da manufar kasa."
- Femi Gbajabiamila

Source: Facebook
Gbajabiamila ya ce Tinubu bai tunanin siyasa
Tsohon shugaban majalisar wakilan ya ce wadannan matakai ba na siyasa ba ne, domin shugaba mai son lashe zabe ba zai dauki irin wadannan matakai masu wahala ba.
"Wannan ba aikin dan siyasa mai tunanin zaben gaba ba ne. Aikin jarumin shugaba ne wanda ke da damuwa kan makomar ’yan Najeriya da kuma al’ummar da za ta gaje mu."
- Femi Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila ya amince cewa wadannan gyare-gyare na kawo wahala ga jama’a a halin yanzu, amma ya bukaci ’yan kasa da su yi hakuri, don za a moriyarsu a nan gaba.
Shugaba Tinubu ya ba Izalah tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gwangwaje kungiyar Izalah reshen jihar Gombe da tallafi.
Shugaba Tinubi ya bada gudunmawar N10m ga kungiyar, don su ci gaba da inganta ayyukansu.
Mai girma shugaban kasan ya yaba da irin gudunmawar da kungiyar take ba shi a gwamnatinsa, wadda ya ce ko kadan ba zai manta ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

