Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Harama, Nan ba da Jimawa ba Za a Daina Dauke Wuta a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa nan ba da jimawa ba yan Najeriya za su ga an daina dauke wutar lantarki kwata-kwata
- Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati ta kamo hanyar samar da wutar da ake bukata a Najeriya
- An kaddamar da azuzuwan horarwa biyar da dakunan kwanan dalibai a Cibiyar Horas da Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Najeriya ta kamo hanyar zuwa matakin samar da wutar lantarkin da ba za a rika daukewa ba.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a Abuja yayin kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Horas da Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya (NAPTIN).

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin ayyukan da aka kaddamar a NAPTIN akwai dakunan horarwa guda biyar da gidan kwanan dalibai mai dakuna 104.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adelabu ya ce wannan sababbin gine-gine sun shiga tarihi a cibiyar kuma za su taimaka wajen kara inganta bangaren makamashi a Najeriya
Najeriya za ta samar da wuta mara yankewa
A cewarsa, wannan aiki da aka kammala ya kara tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu mai fada da cikawa ce, tana aiwatar da abin da ta yi alkawari.
Ministan ya ce ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi ya fara haifar da sakamako mai kyau domin wutar Lantarki da ake samarwa yanzu ta zarce ta baya.
"Nan ba da jimawa, za a samar sa wutar lantarki babu yankewa, za daina dauke wuta atsawon wanni 24 na kowace ranar mako. Wannan abu ne da zai yiwu kuma mun fara ganin alamu."
Ministan ya ce gwamnati na samar da hasken wutar lantarki a jami’o’i, asibitocin koyarwa, cibiyoyin kiwon lafiya, hukumomin gwamnati da garuruwa.
Najeriya za ta iya kera kayan wuta a gida
Adebayo Adelabu ya jaddada cewa wuta ita ce ginshiƙi ga ci gaban sauran muhimman sassan tattalin arziki kamar ilimi, lafiya da sufurin jiragen sama.
“Muna da duk abin da ake bukata domin fara kera na’urorin auna wuta, wayoyi, transufoma, da manyan batura a nan cikin gida, za a yi gagayya da mu a duniya nan gaba.
Muna da kwakwalwa, muna da mutane masu hazaka, dole mu dogara da kanmu, kuma muna dab da cimma hakan.”
- In ji Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu.
Adelabu ya ce sababbin wuraren horaswar da aka gina sun tabbatar da kudirin gwamnati na samar da kwararrun ma’aikata da za su iya shawo kan kalubale a bangaren makamashi.

Source: Facebook
NAPTIN ta hango haske a goben Najeriya
Shugaban NAPTIN, Ahmed Nagode, ya bayyana cewa wannan aikin wani tubali ne da zai haskaka makomar bangaren wutar lantarki a Najeriya, Premium Times ta rahoto.
Ya ce cibiyar na da shirin kulla haɗin gwiwa domin aiwatar da shirin Next Generation Rescue Programme da zai horar da matasan Najeriya tare da ba su dama.
Tushen wutar lantarki ya lalace a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa babban tushen wutar lantarkin Najeirya ya lalace karo na farko a wannan shekarar ta 2025.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tushen wutar ya lalace ne da misalin ƙarfe 11:23 na safiyar ranar Laraba, lamarin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasa.
Bayanan da aka tattara daga ISO sun nuna cewa ƙarfin wutar da ake samarwa ya ragu daga 2,917.83MW zuwa 1.5 MW kacal.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


