Trump Ya Dauki 'Yan Najeriya daga Amurka Ya Jibge Su a Wata Kasar Afrika

Trump Ya Dauki 'Yan Najeriya daga Amurka Ya Jibge Su a Wata Kasar Afrika

  • Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya tabbatar da karɓar ‘yan Najeriya da wasu daga Afirka ta Yamma da aka kora daga Amurka
  • Mahama ya ce an fara da mutum 14 da suka hada da ‘yan Najeriya da ɗan Gambia, inda Ghana ta sauƙaƙa musu dawowa ƙasashensu
  • Matakin ya zo ne bayan shirin gwamnatin shugaba Donald Trump na ƙara tsaurara manufofin hana ƙaura zuwa Amurka daga kasashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ghana – Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta amince da karɓar ‘yan ƙasashen Afirka ta Yamma da Amurka ta kora.

Gwamnatin Ghana ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da tsarin yawo cikin ‘yanci a yankin ECOWAS na wasu watanni ba tare da biza ba.

Trump da shugaba Bola Tinubu na Najeriya
Donald Trump da shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton BBC ya nuna cewa Mahama ya ce an riga an karɓi rukuni na farko da ya kunshi mutane 14, daga cikinsu akwai ‘yan Najeriya da ɗan Gambia.

Kara karanta wannan

Tinubu: Sai da rajistar haraji za a yi hulda da banki a Najeriya daga 2026

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin tura mutane Ghana daga Amurka

Mahama ya ce gwamnatin sa ta amince da shirin ne saboda manufofin haɗin kan ECOWAS da suka bai wa ‘yan ƙasashen yankin damar shiga Ghana ba tare da biza ba har tsawon kwana 90.

Ya ce kasancewar ‘yan Afirka ta Yamma na da ‘yancin shiga Ghana ya sa ba za a ga matakin a matsayin cin zarafi ba, domin kowane ɗan yankin na iya samun matsuguni na ɗan lokaci.

Ya ce Ghana ta riga ta shirya don taimakawa sauran da Amurka za ta aiko daga cikin ƙasashen yankin, inda gwamnati za ta ci gaba da sauƙaƙa musu dawowa gida.

Ghana ta dawo da 'yan Najeriya gida

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutum 14 da suka isa Accra, Ghana kasar ta tabbatar da jigilar ‘yan Najeriya zuwa ƙasarsu.

Punch ta wallafa cewa an fara taimaka wa ɗan asalin Gambia domin ya samu hanyar komawa gida daga kasar Ghana.

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta ja daga, ta ba gwamnatin Tinubu kwanaki 14 ta janye harajin fetur

Mahama ya bayyana wannan mataki a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da Ghana ke amfani da su wajen bin ƙa’idar ɗan’adamtaka da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Tsauraran manufofin Trump a Amurka

Tun lokacin da Shugaba Donald Trump ya hau mulki, gwamnatin Amurka ta ƙara tsaurara dokokin shige da fice tare da korar dubban bakin haure zuwa ƙasashen da ba nasu ba.

An ruwaito cewa a watan da ya gabata an mayar da mutane bakwai zuwa Rwanda, sannan wasu biyar zuwa Eswatini da takwas zuwa Kudancin Sudan.

Shugaban Ghana da da Bola Tinubu na Najeriya
Shugaban Ghana da da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Duk da wannan tsari, Mahama ya bayyana dangantakar Ghana da Amurka a matsayin mai cike da ƙalubale, musamman bayan ƙara haraji ga kasar da ƙuntata samun takardun biza.

Sai dai ya ce duk da hakan, dangantakar ƙasashen biyu na ci gaba da kasancewa mai kyau, inda suka ci gaba da tattaunawa kan batutuwan siyasa da tattalin arziki.

An kashe mutumin Trump a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun harbe wani matashi da ke da alaka da Donald Trump a Amurka.

An kashe matashin ne mai suna Charlie Kirk yayin da ya ke jawabi ga dalibai a wata jami'a a gaban matarsa da 'ya'yansa.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fadi tsoron da APC ta ji bayan kai wa 'yan adawa hari a wajen ibada

Shugaba Donald Trump na Amurka da Benjamin Netanyahu sun yi Allah wadai da kashe matashin da aka yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng