NiMet: Bayan Kusufin Wata, za a Yi Guguwa da Ruwa a Kano, Wasu Jihohin Arewa
- Hukumar NiMet ta fitar da hasashen cewa za a samu ruwan sama mai dauke da guguwa a jihohin Arewa da dama a ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025
- A Arewa ta Tsakiya, an hango yiwuwar ruwan sama tun da safe a wasu jihohi, sannan da rana da yamma za a samu ruwan sama mai yawa
- A Kudancin Najeriya, sama za ta kasance da gajimare tare da ruwan sama mai ɗan sauƙi da safe, amma daga baya ruwan sama mai tsanani zai sauka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NiMet, ta bayyana yadda yanayi zai kasance a ranar Litinin 8 ga watan Satumba, 2025.
Hukumar ta yi gargadin cewa za a samu ruwan sama da guguwa a sassan Arewa da kuma Kudancin ƙasar nan.

Source: Original
Rahoton da NiMet ta fitar a X ya nuna cewa jihohi da dama za su fuskanci ruwan sama tun daga safiya, yayin da wasu za su ci gaba da fuskantar guguwar iska da ruwan sama da yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NiMet ta kuma shawarci al’umma musamman mazauna wuraren da ake fama da ambaliya da su kasance cikin shiri don guje wa haɗura da asarar rayuka ko dukiya.
Hasashen yanayi a Arewacin Najeriya
A safiyar Litinin, NiMet ta ce ana sa ran samun gajimare tare da fitowar rana lokaci zuwa lokaci a sassan Arewacin Najeriya.
Rahoton hukumar ya nuna cewa a jihohin Taraba da Adamawa, matsakaicin ruwan sama zai sauka tun da safe.
Da rana zuwa yamma, jihohin Borno, Sokoto, Kebbi, Yobe, Gombe, Bauchi, Kaduna, Adamawa, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara da Taraba za su fuskanci guguwa mai ɗauke da ruwan sama.
Hasashen yanayi a sauran jihohin Arewa
Da safiya, rahoton ya nuna cewa akwai yiwuwar samun ruwan sama a sassa na Abuja (FCT), Nasarawa, Benue, Niger da Kogi.
Sai da rana da yamma ne NiMet ta hango ruwan sama mai yawa da guguwar iska a jihohin Nasarawa, Niger, Plateau, Kogi, Kwara, Benue da kuma Abuja.
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
A yankin Kudu, NiMet ta bayyana cewa za a fara da gajimare da ruwan sama mai sauƙi a jihohin Enugu, Ebonyi, Imo, Abia, Cross River da Akwa Ibom.
Daga baya da rana da yamma, ruwan sama mai yawa zai sauka a jihohin Oyo, Ondo, Osun, Ekiti, Lagos, Edo, Delta, Enugu, Ebonyi, Abia, Imo, Anambra, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Source: Getty Images
NiMet ta gargadi al’ummar Najeriya
Hukumar ta ja hankalin jama’a da cewa guguwar iska na iya haifar da matsaloli a hanya tare da kawo cikas ga harkokin jama'a.
Haka kuma, ta gargadi mazauna wuraren da ke fama da ambaliya da su kasance cikin shiri don gujewa bala’i.
NiMet ta jaddada cewa wannan hasashe na nufin tallafa wa jama’a wajen shirin kare kansu, kayansu da kuma harkokin yau da kullum daga illolin yanayi.
Legit ta tattauna da Aminu
Wani matashi a jihar Gombe, Aminu Baba ya zantawa Legit Hausa cewa an yi ruwa a ranar Litinin kamar yadda NiMet ta yi hasashe.
Aminu ya ce:
"An yi ruwan sama a ranar Litinin, sai dai babu guguwa kamar yadda aka ce za a yi. Hakan ya nuna masu hasashen sun dace."
Wata ya yi kusufi a kasashen duniya
A wani rahoton, kun ji cewa a daren Lahadi, 7 ga watan Satumba 2025 wata ya yi kusufi a wasu kasashen duniya.
Najeriya na daga cikin kasashen duniya da dama da aka bukaci al'umma su zauna da shirin yin addu'a.
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Saudiyya ta bukaci 'yan kasarta da su fita salla a masallacin Harami da karfe 9:00 na dare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


