Dattawan Arewa Sun Cimma Matsaya kan Rashin Tsaro, Sun Sanar da Shugaba Tinubu

Dattawan Arewa Sun Cimma Matsaya kan Rashin Tsaro, Sun Sanar da Shugaba Tinubu

  • Kungiyar dattawan Arewa watau NEF ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaron da ta dade tana addabar yankin
  • Manyan na Arewa sun koka kan yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka ta hanyar kashe mutane da raba su da matsugunansu
  • Sun ba da shawara ga Mai girma Bola Tinubu kan matakin da ya kamata a dauka don a samu zaman lafiya a yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dattawan Arewa a karkashin kungiyar Northern Elders Forum (NEF), sun ba mai girma Bola Tinubu shawara kan matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin.

Dattawan na Arewa sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a Arewacin Najeriya, saboda matsalar rashin tsaro wadda ta durkusar da tattalin arzikin yankin.

Dattawan Arewa sun bukaci a sanya dokar ta baci
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wurin wani taro a Japan Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar NEF, Farfesa Abubakar Jiddere, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Kungiyar NEF ta nuna damuwa matuka kan yawaitar hare-hare, garkuwa da mutane da kisan jama’a a fadin yankin Arewa.

Ta yi gargadin cewa idan ba a ayyana dokar ta-baci ba, hakan na iya haifar da daukar doka a hannu, rikice-rikice wadanda za su zama barazana ga zaman lafiyar Najeriya da kwanciyar hankali.

NEF ta jaddada cewa idan gwamnatin tarayya ta kasa yin abin da ya kamata, hakan zai lalata hadin kan kasa, dorewar dimokuradiyya, daidaiton siyasa da zaman lafiya a yankin.

A bisa hakan sai ta bukaci gwamnatin Tinubu, gaggauta ayyana dokar ta-baci bisa ga kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa da kasa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, rahoton The Nation ya tabbatar.

An kawo misalan hare-haren 'yan bindiga

Kungiyar ta tunatar da cewa a ranar 19 ga watan Agusta an kai mummunan hari a masallacin Unguwan Mantau, inda ‘yan bindiga suka kashe sama da mutane 27 da ke Sallar Asuba tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Likitoci sun shata wa gwamnatin Tinubu layi, za su dauki mataki a cikin kwanaki 10

Kungiyar ta kuma jawo hankali kan kisan gilla da aka yi wa mutane 35 da aka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara duk da biyan kudin fansa.

Hakazalika ta kuma bayyana hare-hare guda biyu da aka kai a kananan hukumomin Kauru da Kudan jihar Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas tare da jikkata wasu mutum takwas.

Dattawan Arewa sun ba Tinubu shawara
Hoton shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Wadanne bukatu dattawan suka gabatar?

"Ayyana dokar ta-baci a Arewacin Najeriya shi ne zai tabbatar da amincewa akwai wannan gagarumar matsalar."
"A tura jami’an tsaro da suka samu horo mai kyau, masu makamai da kayan aiki yadda ya kamata, tare da ba su ka’idojin yaki da suka dace domin kare al’ummomi da kuma tsare yankunan kan iyaka na kasa da kasa."
"A samar da wadatacciyar diyya, sake tsugunarwa da tallafin jin kai ga wadanda suka tsira da wadanda aka raba da muhallansu, bisa ka’idojin jin kai na kasa da kasa."

- Abubakar Jiddere

Gwamna Dauda ya magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana kalubalen da yake fuskanta wajen magance matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin NEMA, Ambaliya ta afka wa dubban mutane a Adamawa

Gwamna Dauda ya bayyana cewa rashin ikon da yake da shi a kan jami'an tsaro, ya sanya ya gaza kawo karshen matsalar tsaro.

Ya nuna cewa yana da masaniya kan inda 'yan bindiga suke buya amma rashin iko ne babban abin da ke kawo masa cikas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng