Ga Masu Burin Arziki: Dangote Ya Fadi Yadda Ya Tara Dukiya ba Tare da Cin Gado ba
- Alhaji Aliko Dangote ya ce dukkan arzikin da yake da shi yanzu ya gina shi ne daga tushe ba tare da gado daga mahaifinsa ba
- Ya bayyana cewa duk wani abu da ya gada daga mahaifinsa ya raba shi tun kafin ya yi karfi a wajen harkokin kasuwanci
- Dangote ya ce ya fara sana’a da saye da sayar da siminti a Legas, daga nan ya fadada harkokinsa zuwa wasu masana’antu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba gado daga iyayensa ya dogara da shi wajen kafa ginshiƙin kamfaninsa ba.
Aliko Dangote da dan asalin jihar Kano ne a Najeriya, shi ne wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi Janairun 2020, wacce ta sake bayyana a yanar gizo kwanan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hirar, Aliko Dangote ya yi bayani kan asalinsa da kuma yadda ya fara harkokin kasuwanci daga tushe.
Tarihin dangin Aliko Dangote
Dangote ya bayyana cewa kakansa, Alhaji Sanusi Dantata, shi ne mafi arziki a Yammacin Afirka a shekarun 1940.
Haka kuma ya ce mahaifinsa, kodayake attajiri ne a harkokin siyasa da kasuwanci, bai ci gajiyar dukiyar da ya bari ba.
Ya ce ya fi alfahari da cewa ya samo dukiyar da yake da ita a yau ne da guminsa da kuma gina kasuwanci ba daga cin gado ba.
Farkon harkar kasuwancin Dangote
Dangote ya fara aikinsa ne tare da kawunsa kafin daga bisani ya tafi Legas, inda ya tsunduma cikin harkar saye da sayar da siminti.
Rahoton The Nation ya nuna cewa ya ce siminti muhimmin bangare ne wajen gina abubuwan more rayuwa, wanda Najeriya da Afirka gaba ɗaya ke bukata.
Wannan ne ya sa ya zuba jari sosai wajen kafa masana’antar siminti, wanda a wancan lokacin an fi shigowa da shi daga ƙasashen waje.
Dabarar zuba jari da Dangote ya yi
Dangote ya ce rashin wadatar gidaje a Najeriya ne ya sa ya fahimci bukatar masana’antar siminti mai ƙarfi a cikin gida.
Daga nan ne ya fara fadada harkokinsa zuwa sauran sassa na kasuwanci a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Ya ce wannan dabarar ta taimaka wajen rage dogaro da shigo da kaya daga kasashen waje da kuma bunkasa tattalin arzikin gida.
Wasu nasarorin da Dangote da ya samu
Dangote Group na daga cikin manyan kamfanonin Afirka da ke da rassa fiye da 15 a kasashe akalla 10 na nahiyar.
Kamfanonin da ke karkashin kulawar attajirin sun hada da kamfanonin siminti, sukari, matatar mai da sauransu a ciki da wajen Najeriya.

Source: UGC
Dangote zai kafa kamfani a Habasha
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote na shirin kafa kamfanin takin zamani a kasar Habasha.
Binciken da Legit Hausa ta yi ya nuna cewa za a kashe Dala biliyan 2.5 wajen kafa kamfanin domin wadata kasar ta taki.
Rahoto ya nuna cewa a makon da ya wuce ne kamfanin Dangote da kasar Habasha suka rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da kamfanin.
Asali: Legit.ng

