NiMet Ta Yi Hasashen Ruwa da Guguwa a Kano, Gombe da Wasu Jihohin Arewa

NiMet Ta Yi Hasashen Ruwa da Guguwa a Kano, Gombe da Wasu Jihohin Arewa

  • Hukumar NiMet ta bayyana cewa za a sami guguwar dauke da ruwan sama a sassan Arewa a yau Asabar
  • A Kudu kuwa, an yi hasashen ruwan sama mai sauƙi a wasu jihohi musamman daga yamma zuwa dare
  • NiMet ta gargadi al’umma musamman masu zaune a wuraren da ake fama da ambaliya da kuma direbobi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen yanayin yau Asabar, 30 ga watan Agusta, 2025, inda ta yi hasashen ruwan sama da guguwa a wurare da dama.

Rahoton ya nuna cewa jihohin Arewa za su fi fuskantar ruwan sama mai ɗauke da guguwa musamman a safiya da kuma daga yamma zuwa dare.

Wata mata na tafiya yayin da ake ruwam sama
Wata mata na tafiya yayin da ake ruwam sama. Hoto: BGetty Images
Source: Getty Images

A sakon da ta wallafa a X, hukumar ta ce yanayin zai shafi harkokin sufuri da rayuwar al’umma a wasu sassan kasar.

Kara karanta wannan

Jerin ayyukan Naira tiriliyan 3.9 da aka amince a yi a Lagos a shekara 2 na Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NiMet: Za a yi ruwa a jihohin Arewa

A safiyar yau Asabar, NiMet ta bayyana cewa za a sami guguwa da ruwan sama a jihohin Kebbi, Zamfara, Kano, Katsina, Kaduna, Sokoto, Taraba da Jigawa.

A cewar hukumar, wannan yanayi zai iya kawo tsaiko ga harkokin sufuri da kuma noman gonakin yankunan.

Daga yamma zuwa dare, ana sa ran guguwa da ruwan sama a Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Yobe da Borno.

Hakan na iya haifar da matsala ga al’ummomi da ke cikin karkara musamman masu dogaro da hanyoyin mota.

Hasashen yanayi a Arewa ta Tsakiya

Da safiya, rahoton ya ce za a samu ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan jihohin Niger, Nasarawa da Plateau da Abuja (FCT).

Yanayin zai iya sauya wa zuwa ruwan sama matsakaici daga yamma zuwa dare a jihohin Nasarawa, Benue, Kwara, Niger, Plateau, Kogi da kuma babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil

NiMet ta ce ya kamata masu sufuri da kuma manoma su kula, domin ruwan zai iya kawo tangarda ga lamura.

Yadda ruwa ya jawo ambaliya a Mokwa, jihar Neja
Yadda ruwa ya jawo ambaliya a Mokwa, jihar Neja. Hoto: Muhammad Bello Mokwa
Source: Facebook

Hasashen yanayi a jihohin Kudu

A safiyar yau, jihohin Ondo, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom za su fuskanci gajimare tare da ruwan sama mai sauƙi.

Yanayin zai cigaba a wasu jihohi daga yamma zuwa dare inda ake sa ran ruwa a Ondo, Ekiti, Osun, Edo, Abia, Imo, Oyo, Ebonyi, Enugu, Ogun, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Rivers, Bayelsa.

Wannan na iya sanyaya yanayi amma kuma yana iya kawo cikas ga harkokin sufuri da kasuwanci musamman a manyan birane.

NiMet ta gargadi jama'ar Najeriya

NiMet ta gargadi al’umma da su yi taka-tsantsan yayin guguwa saboda iska mai karfi na iya rushe bishiyoyi, shinge da kuma kawo hatsari ga masu tuƙi.

Hukumar ta kuma shawarci masu sufuri da su guji tafiya yayin ruwan sama mai yawa domin gujewa hadura.

NiMet ta yi hasashen ruwa na kwana 3

A wani rahoton kun ji cewa hukumar hasashen yanayi ta kasa, NiMet ta fitar da sanarwa kan kwanaki da za a shafe ana ruwa.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sheka ruwan sama a Kano, Neja da wasu jihohin Arewa 14 ranar Juma'a

Hukumar ta bayyana yankunan da za a shafe kwanaki ana ruwan tare da gargadin cewa yanayin zai iya jawo ambaliya.

NiMet ta bukaci ta bukaci 'yan Najeriya su saurari dukkan matakan kariya da hukumomi suke bayarwa domin kubutar da rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng