Arziki Zai Karu: Dangote zai Kafa Katafaren Kamfanin Taki na $2.5bn a Habasha
- Aliko Dangote ya kulla yarjejeniya da gwamnatin Habasha kan gina babbar masana’antar takin zamani a birnin Gode
- Masana’antar za ta kasance cikin mafi girma a duniya, kuma za ta samar da tan miliyan uku na takin urea a duk shekara
- Yarjejeniyar ta bai wa Dangote kashi 60 cikin 100, yayin da gwamnatin Habasha ta mallaki kashi 40 na masana'antar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shahararren ɗan kasuwa kuma attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya cimma yarjejeniya da gwamnatin ƙasar Habasha don gina kamfanin takin zamani.
An rattaba hannu a kan yarjejeniyar ne tsakanin kamfanin Dangote da hukumar zuba jari ta Habasha (EIH).

Source: Twitter
Legit Hausa ta gano cewa Firaministan Habasha, Abiy Ahmed ne ya wallafa bayanai kan yarjejeniyar a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban aikin zai kasance a yankin Somali a garin Gode, kuma yana ɗaya daga cikin manyan matakan da ƙasar Habasha ke ɗauka domin tabbatar da isasshen abinci da sauya harkar noma.
Abubuwan da yarjejeniyar Dangote ta ƙunsa
Dangote zai mallaki kaso 60 cikin 100 na hannun jarin kamfanin da za a gina a kan $2.5bn, yayin da gwamnatin Habasha ta hanyar EIH za ta rike kaso 40.
An tsara cewa masana’antar za ta kammalu cikin wata 40, tare da samar da bututun iskar gas daga gonakin Calub da Hilala.
EIH ta bayyana cewa za a samar da tan miliyan uku na taki urea a duk shekara, wanda hakan zai sanya wannan masana’anta cikin biyar mafi girma a duniya.
Haka kuma, akwai tanadin fadada kamfanin zuwa samar da takin zamani na sinadarin ammonia a nan gaba.
Kalaman Habasha da kamfanin Dangote
Shugaban hukumar EIH, Dr Brook Taye, ya ce wannan mataki babban cigaba ne a tafiyar Habasha wajen dogaro da kai da kuma inganta harkar noma.
Punch ta wallafa cewa Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya yaba da yarjejeniyar, inda ya ce:
“Wannan babbar masana’anta za ta samar da tan miliyan uku na takin zamani a kowace shekara, abin da zai sanya Habasha cikin jerin ƙasashe mafi girma wajen samar da takin zamani a duniya.”
Ya ƙara da cewa wannan aikin zai samar da dubban ayyukan yi, rage dogaro da shigo da taki daga waje, da kuma tabbatar da ingantattun kayayyakin gona ga manoma.

Source: Getty Images
A nasa jawabin, Alhaji Aliko Dangote ya ce zuba jarin da ya yi a kasar ya dace da hangen nesansa na ganin Afirka ta samu ci gaban masana’antu.
Ya ce:
“Mun kuduri aniyar yin amfani da kwarewarmu a manyan ayyukan masana’antu don tabbatar da wannan aiki ya zama ginshiƙi na sauyin masana’antu a Habasha da kuma inganta noma.”
Tasirin aikin ga Habasha da Afirka
Ana sa ran masana’antar za ta taimaka wajen rage dogaro da shigo da taki daga waje, ta hanyar samar da isasshen taki ga manoma a cikin gida da kuma fitar da shi zuwa Gabashin Afirka.
A cewar masana tattalin arziki, wannan mataki zai inganta tattalin arzikin Habasha, ya kara samar da ayyukan yi, tare da samar da hanyar samun kudin shiga daga fitar da taki.
Dangote ya kara farashin man fetur
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote da wasu 'yan kasuwa sun kara farashin man fetur a Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kamfanin mai na A.A Rano na cikin wadanda suka kara farashin a makon da ya wuce.
Masana harkar man fetur sun bayyana cewa an samu karin farashin ne saboda sauyawar farashin mai a kasuwar duniya.
Asali: Legit.ng


