"Ba Zai Yiwu ba": Minista Ya Fadi Kuskuren da Tinubu Zai Yi da bai Cire Tallafin Fetur ba

"Ba Zai Yiwu ba": Minista Ya Fadi Kuskuren da Tinubu Zai Yi da bai Cire Tallafin Fetur ba

  • Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kare matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na cire tallafin fetur
  • Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa da shugaban kasan ya ci gaba da biyan tallafin fetur, da tabbas ya yi wa doka hawan kawara
  • Ministan ya nuna cewa gwamnatin yanzu tana amfani da kudin da ake biyan tallafin, wajen aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai iya ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.

Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai iya ci gaba da biya ba, domin babu tanadin hakan a cikin kasafin kuɗi a lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki.

Ministan Tinubu ya kare matakin cire tallafinan fetur
Hotunan shugaban kasa, Bola Tinubi da ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: @DOlusegun, @BTOofficial
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce Ministan ya bayyana hakan ne yin da yake jawabi a ranar Litinin a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA).

Kara karanta wannan

Duk da yana Brazil, Shugaba Tinubu ya yi magana kan hatsarin jirgin kasan Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba dai, a ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur.

Minista ya kare Tinubu kan cire tallafin fetur

Tunji-Ojo ya ce biyan tallafin ba tare da amincewar majalisa ba ya saba doka.

"A lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, babu wani tanadi na tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin kasa."
“Biyan tallafin zai kasance abin da ya sabawa doka saboda ba a saka shi a kasafin kuɗi ba. Mun tattara kurakurai da aka yi tsawon shekaru da dama, yanzu kuma ana gyara su."
"Saboda haka, dole ne mu kawar da son zuciya a gefe, mu kalli gaskiya daga inda muka fito da kuma inda muke yanzu.”

- Olubunmi Tunji-Ojo

Olubunmi Tunji-Ojo ya ce dole ta sa a cire tallafi

Sai dai Tunji-Ojo ya ce matakin cire tallafin tilas ne, yana mai jaddada cewa Najeriya tana kashe kusan dala biliyan 25 a kowace shekara wajen biyan tallafi, kuɗin da ya ce ba za a iya ci gaba da biya ba.

Kara karanta wannan

'Abin da ba ku sani ba': Tinubu ya fadi babban abin da ya cimma bayan hawa mulki

Tunji-Ojo ya kare Tinubu kan cire tallafin man fetur
Hoton ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: @BTOofficial
Source: Twitter
"Mun kasance muna kashe kuɗin da ba mu da su. Idan mutum na da kari a jiki, ba a ba shi Panadol ba. Tiyata ce mafita."
"Tattalin arziki ba wawa ba ne, amma matakan da muka dauka na tsawon shekaru su ne wawanci."

- Olubunmi Tunji-Ojo

Ministan ya ce adadin kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin ana karkatar da su yanzu zuwa manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa.

Tinubu ya kadu kan hatsarin jirgin kasan Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna kaduwaraa kan hatsarin jirgin kasan da ya auku a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Shugaba Tinubu ya bayyana hatsarin a matsayin abin damuwa, inda ya yi addu'a ga iyalan fasinjojin da lamarin ya ritsa da su.

Mai girma Bola Tinubu ya ba da tabbacin cewa za a dauki matakan da suka dace domin sake aukuwar irin hakan a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng