Gwamnatin Katsina Ta Dauki Matakin Fuskantar Matsalar 'Yan Bindiga
- Gwamnatin Katsina ta nuna damuwarta kan hare-haren 'yan bindiga da suka addabi wasu sassan jihar
- Mukaddashin gwamnan jihar Katsina ya bayyana cewa sun sayo sababbin motocin yaki masu sulke
- Malam Faruk Lawal Jobe ya ba da tabbacin cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda ta sayo sababbin motocin yaki masu sulke.
Gwamnatin ta sayo motocin ne domin kara karfin aiki da inganta motsin jami’an tsaro a cikin yankunan jihar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga.

Source: Facebook
Mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, shi ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da hadimin Gwamna Radda ya sanya a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Katsina ta damu kan rashin tsaro
Ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman bayan hare-haren da aka kai a Gidan Mantau, unguwar Karfi, ƙaramar hukumar Malumfashi, inda ‘yan bindiga suka kashe masallata da dama.
Yayin da yake magana bayan taron majalisar tsaron jihar da aka gudanar da yammacin Asabar, mukaddashin gwamnan ya bayyana harin a matsayin “abin bakin ciki kuma abin takaici.
Sai dai, ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayuka.
Ya bayyana manyan jarin da gwamnatin jihar ta saka a fannin tsaro, ciki har horas da jami’an tsaro, da kuma ƙarfafa shirin tsaron al’umma, musamman ta hanyar C-Watch da kungiyoyin yan sa-kai.
Ya ce waɗannan ayyuka sun yi nasarar tsare kananan hukumomi hudu daga cikin takwas da ke sahun gaba wajen fuskantar barazanar ‘yan bindiga. Waɗannan ƙananan hukumomi sun haɗa da: Jibia, Batsari, Safana, da Dan Musa.
"Yaki da ‘yan bindiga ba zai ƙare ba sai mun ci nasara. Ba za mu bari ayyukan tsoro na waɗannan miyagu da ke kai wa talakawa hari da safe su karkatar da mu ba."
"Muna yaba wa jarumtakar al’umma da suka tsaya tsayin daka, suka maida martani, suka kuma ci galaba a kansu, abin da ya sa kokarinsu na tarwatsa zaman lafiya ya ci tura.”
- Farouk Lawal Jobe

Source: Facebook
An ceto mutanen da aka sace a Katsina
Mukaddashin Gwamnan ya tabbatar da cewa an ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su a safiyar Asabar, ban da waɗanda suka tsere da kansu a lokacin da ake kokarin sace su.
Haka kuma, ya bayyana ‘yan majalisar tarayya sun gana da hafsan hafsoshi da kuma hafsan sojojin kasa domin samar da karin jami’ai da kayan aiki ga jihar.
Ya sanar da cewa hafsan sojojin kasa zai kai ziyara Katsina ranar Lahadi domin duba halin da ake ciki a filin daga.
Abin a yaba ne
Aisha Kabir mazauniyar jihar Katsina ta shaidawa Legit Hausa cewa matakin da gwamnatin ta dauka abin a yaba ne.
"Wannan abin a yaba ne. Ya nuna kokarin gwamnati wajen ganin ta samar da tsaro ga al'umma."
"Sai dai, ba sayo motoci kawai ake bukata ba, ya kamata gwamnati ta tashi ta nuna da gaske take yi wajen samar da tsaro."
- Aisha Kabir
Gwamnatin Katsina ta bukaci a fito rajistar katin zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta bukaci mutane su fito don yin rajistar katin zabe.
Ta bayyana cewa yin rajistar yana da matukar muhimmanci domin samun damar shiga zabukan da ke tafe a nan gaba.
Gwamnatin ta kuma shawarci wadanda suka riga suka yi rajistar da ka da su sake yi don gujewa maimaitawa.
Asali: Legit.ng


