Mamakon Ruwan Ya Lalata Gidaje, Ya Raba Mutane sama da 600 da Muhallansu a Yobe
- Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya gigita wasu mazauna jihar Yobe bayan rugujewar gidaje aƙalla 612 a wurare da dama
- Unguwannin da ke kusa da kwari ne suka fi fuskantar matsala a sakamakon ambaliyar da ta afku a ranar Juma'a
- Mazauna yankunan sun ce dama sun dade suna fama da matsalar ambaliya saboda rashin magudanan ruwa a kusa da su
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe –Ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a daren Juma’a ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa a garin Potiskum, a jihar Yobe.
Lamarin da ya jawo rushewar gidaje da dama tare da raba mazauna fiye da 612 da matsugunnansu.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafin Facebook, Shugaban SEMA na jihar, Mohammed Goje ya ce wuraren da suka fi fuskantar matsalar su ne yankuna da ke kusa da koguna da kwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wuraren da ambaliya ta yi ƙamari a Yobe
Daily Trust ta ruwaito cewa wuraren da su ka fi fuskantar matsala saboda ambaliya sun haɗa da Arikime, Ramin Kasa, Tandari, Nahuta, Boriya, Rugar Fulani, da Unguwar Kuwait.
Sauran wuraren da ambaliyar ta shafa sun haɗa da Old Prison, Filin Nashe, Unguwar Makafi/Majema da Unguwar Jaji Bakin Kwari.

Source: Original
Sai kuma unguwanni da su ka haɗa da Afghanistan, Tsangaya Bakin Kwari, Karofi, Bayan Garejin Danjuma da bayan Fudiyya Potiskum.
Mazauna waɗannan unguwannin sun dade suna fama da irin wannan matsalar saboda rashin ingantattun hanyoyin magudanan ruwa.
Jama'a sun shiga mawuyacin hali a Yobe
Wani mazaunin yankin mai suna Musa Adamu ya bayyana wa jaridar yadda dinka tsinci kansu a cikin mawuyacin yanayi.
Ya ƙara da cewa:
“Gidaje da dama sun rushe, amma babu wanda ya rasa ransa. Yawancin waɗanda abin ya shafa suna cikin sansanonin ’yan gudun hijira, yayin da wasu kuma suka koma wurin danginsu.”

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
Matakin da gwamnatin Yobe ta ɗauka
Tuni hukuma SEMA a jihar Yobe ta bayyana cewa an fara ɗaukar matakan taimakon mutanen da iftila'in ambaliyar ta faɗa wa.
Mohammed SEMA ya bayyana cewa:
“SEMA ta tura tawagarta ta filin don tantance halin da ake ciki. Abin farin cikin shi ne, babu wanda ya rasa ransa.”
“Ana ci gaba da yin cikakken bincike a halin yanzu, kuma gwamnati ta yi alkawarin samar da tallafin gaggawa na ceton rai."
Ya tabbatar da cewa Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da umarnin a agaza wa mutanen, sannan a tabbata an ɗauki matakan kariya don gaba.
Yobe: Ana hasashen ambaliya a wasu jihohi
A baya, kun ji hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da sabon gargadi ga kan yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli na shekarar 2025
A cewar rahoton hasashen yanayi na kakar ruwa (SCP), an gano cewa akwai wasu yankunan Arewa da Kudancin ƙasar nan da ke cikin barazanar ambaliya.
Daga cikin jihohin akwai Yobe, Sokoto da Neja, Adamawa da Kaduna wacce ta ke kan gaba a jerin wuraren da ke fuskantar haɗarin gaske, inda ta nemi a ɗauki mataki.
Asali: Legit.ng
