Minista Ya Kwararo Yabo ga Tinubu, Ya Bayyana Fannin da Ya Yi Wa Magabatansa Zarra
- Karamin ministan ayyuka, Bello Goronyo, ya yaba kan yadda Shugaba Bola Tinubu yake ba da muhimmanci ga fannin abubuwan more rayuwa
- Ministan ya bayyana cewa babu shugaban kasa daga cikin wadanda suka gabata, da ya ba da irin wannan muhimmancin kamar Tinubu
- Bello Goronyo ya nuna cewa kowane yanki na kasar nan na amfana da ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu take gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Karamin ministan ayyuka, Bello Goronyo, ya bayyana bangaren da Shugaba Bola Tinubu, ya yi wa shugabannin da suka gabata fintinkau.
Bello Goronyo ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa cikin shekaru 40 da ya ba gina hanyoyi da gadoji muhimmanci kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja tare da shugaban hukumar kula da hanyoyin tarayya (FERMA), kungiyar masu motocin sufuri ta Najeriya (NARTO), da kungiyar IPMAN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Bello Goronyo ya ce kan Shugaba Tinubu?
Bello Goronyo ya ce Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta gyara manyan gadoji da ke da matsala a faɗin kasar nan, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da hakan.
Ya bayyana cewa cikin gadojin da za a fara gyarawa da gaggawa akwai gadar Wukari–Jalingo, gadar Mokwa, gadar Gurara, gadar Third Mainland, gadar Carter da sauransu.
Ministan ya ce wannan shirin na da nufin inganta harkokin tattalin arziki da kuma saukaka zirga-zirga a fadin kasar nan.
"Sirrin wannan ci gaba shi ne jajircewar shugaban kasa da goyon bayansa ba tare da gajiyawa ba."
"A cikin shirinsa na Renewed Hope Agenda, samar da ababen more rayuwa shi ne abu na biyar wanda aka fi ba fifiko, wanda shi ne ginshiƙin ci gaba da bunƙasa tattalin arziki."
"Zan iya faɗa ba tare da jin shakku ba cewa babu wani shugaban kasa cikin shekaru 40 da ya ba samar da ababen more rayuwa irin wannan kulawa."
- Bello Goronyo

Source: Twitter
Karamin Ministan ya yabi Dave Umahi
Ya yabawa babban ministan ayyuka, Dave Umahi, bisa yadda ya yi amfani da kwarewarsa a fannin injiniya wajen aiwatar da ayyuka, sannan ya jinjinawa FERMA bisa kokarin ta na kula da hanyoyin tarayya sama da kilomita 36,000 duk da karancin kuɗi.
Ya ƙara da cewa dukkan jihohi 36 sun amfana da gyaran hanyoyi, tare da ayyuka da ke ci gaba a manyan hanyoyi masu muhimmanci kamar Abuja–Lokoja, Abuja–Kaduna–Kano, da Sokoto–Zaria.
Shugaba Tinubu ya magantu kan zabukan cike gurbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan zabukan cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta gudanar a ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2025.
Shugaba Tinubu ya yabawa hukumar INEC kan yadda ta gudanar da zabukan cikin lumana ba tare da wani hargitsi ba.
Hakazalika ya aika da sakon taya murna ga 'yan takarar da suka samu nasara a mazabu daban-daban da aka gudanar da zaben a fadin kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

