Gwamnatin Tinubu Ta Fara Shirin Rage Bashin N4trn ga Kamfanonin Wutar Lantarki
- Majalisar zartarwa ta ƙasa ta fara aiwatar da shirin biyan bashin Naira tiriliyan hudu ga kamfanonin samar da wutar lantarki
- Matakin zai taimaka wajen rage dogon jerin basussukan da suka taru a sashen makamashi, wanda ya dade yana kawo cikas ga samar da wuta
- Kamfanonin samar da wuta sun yi gargadi cewa kudinsu da gwamnatin tarayya ta kwanta a kansu ya na kawo nakasu ga ayyukansu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan kudi kuma ministan da ke kula da tattalin arzikin ƙasa, Wale Edun, ya ce ya gabatar da wata shawara ga majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) kan bashin wutar lantarki.
Ya bayyana cewa ga gabatar da bukatar ne domin bai wa gwamnatin tarayya damar biyan bashin Naira tiriliyan hudu da kamfanonin samar da wutar lantarki ke binta.

Kara karanta wannan
Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Edun ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin hira da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan taron FEC da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati na shirin biyan kudin wuta
Business day ta ruwaito cewa a lokacin taron majalisar, Edun ya gabatar da takardar neman biyan bashin domin samun sahalewar FEC wajen biyan kudin.
Ya ce:
“Na gabatar da jawabi kan muhimmin batun sake fasalin biyan bashin sashen wutar lantarki wanda adadinsa ya kai Naira tiriliyan hudu."
“Ko da yake ba a amince da shirin biyan kudin gaba ɗaya a nan take ba, mun shiga matakin fara biyan kudin da ofishin kula da basussuka (DMO) da sauran kwararru.”
Edun ya bayyana matakin farko na shirin zai kammala cikin makonni uku zuwa hudu, wanda zai zama babban ci gaba wajen shawo kan matsalar bashin.
Kamfanonin wuta na bin gwamnati bashi
A watan Afrilu 2025, kamfanonin samar da wuta (GenCos) sun yi gargadin cewa bashin Naira tiriliyan hudu da su ke bin gwamnatin tarayya ya jefa ayyukansu a tsaka mai wuya.

Asali: Facebook
Rahoton ya nuna cewa cikin bashin, Naira tiriliyan 2 na shekarar 2024 ne, yayin da sauran Naira tiriliyan 1.9 ke daga cikin tsofaffin basussuka da gwamnatin tarayya ba ta biya ba.
A farkon watan Mayu, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin tarayya na iya neman rance domin biyan wani bangare na bashin da ake binsu domin saukaka ayyuka.
Minista: 'Tinubu zai samar da wutar lantarki'
A baya, mun wallafa cewa Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai cika babban alƙawarin da ya ɗauka a lokacin kamfen.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na sane da alkawarin da ta dauka na samar da wadatacciyar wutar lantarki a ƙasar kafin karewar wa’adin Bola Tinubu a shekarar 2027.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki sashen makamashi a matsayin ginshiƙin ci gaban tattalin arzikin ƙasa, saboda haka ba za ta yi wasa da batun samar da isasshiyar wuta ba.
Asali: Legit.ng