Wata Sabuwa: Zanga Zanga Ta Barke a Kaduna, an Ji Abin da Ya Faru

Wata Sabuwa: Zanga Zanga Ta Barke a Kaduna, an Ji Abin da Ya Faru

  • Matasa sun fito kan tituna a jihar Kaduna bayan an zargi jami'an tsaro da wuce gona da iri yayin gudanar da ayyukansu
  • Zanga-zangar dai ta auku ne bayan an zargi jami'an tsaro na rundunar SJTF da hallaka wani matashi har lahira a unguwar Barnawa cikin birnin Kaduna
  • Matasan dai sun toshe hanyoyi tare da kona tayoyi wanda hakan ya jawo cunkoson ababen hawa a yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - An gudanar da zanga-zanga a unguwar Barnawa ta birnin Kaduna da yammacin Litinin, 11 ga watan Agustan 2025.

Zanga-zangar ta barke ne bayan zargin kashe wani matashi da jami’an rundunar hadin gwiwa ta musamman (SJTF), suka yi.

An gudanar da zanga-zanga a Kaduna
Matasa sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An zargi jami'an tsaro da kashe matashi

Jaridar The Cable ta rahoto cewa jami'an rundunar SJTF sun kai samame ne a wani wurin aikata laifuffuka a kusa da kasuwar Barnawa.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina, an ceto mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar SJTF dai wata hukumar tsaro ce da aka kafa domin yaki da laifuffuka a cikin gari da kuma shan miyagun ƙwayoyi.

Rundunar hadin gwiwar na ƙunshe da jami’an sojoji, ‘yan sanda, hukumar tsaron farin kaya (DSS), hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), da kuma hukumar NSCDC.

Bayanai kan lamarin har yanzu ba su fito fili ba, kuma ba a bayyana sunan wanda aka kashe ba a hukumance.

Haka kuma, ba a tabbatar ko wanda aka kashe shi aka nufa kai tsaye ba, ko kuwa harbin ya same shi ne bisa kuskure.

Matasa sun fito kan tituna a Kaduna

Wannan zargin kisan ya tayar da hankalin matasa, inda suka fito a daruruwansu, suka toshe hanyoyi, tare da kunna tayoyi a kan babbar hanyar da ke haɗa Barnawa da sauran sassan birnin Kaduna.

Zanga-zangar ta haifar da gagarumar tangardar zirga-zirgar motoci, lamarin da ya tilasta wa fasinjoji da masu ababen hawa neman wasu hanyoyin daban.

Kara karanta wannan

Jami'an EFCC sun kai samame otel din Obasanjo, an samu bayanai

Masu zanga-zangar sun bukaci a yi adalci ga mamacin, tare da nuna fushinsu kan abin da ya faru.

Daga baya hankula sun kwanta bayan an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.

An yi zanga-zanga a Kaduna
Matasa sun yi zanga-zanga kan kisan wani matashi a Kaduna Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun yi magana kan lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ƙi bayar da ƙarin bayani.

"Eh, mun samu rahoton abin da ya faru, kuma kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin."

- Mansir Hassan

An gudanar da zanga-zanga a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mazauna kauyukan jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwarsu kan matsalar rashin tsaro da ta dade tana ci musu tuwo a kwarya.

Mutanen dai wadanda suka kasance masu yawa, sun fito ne daga kauyuka 30 na gundumomin Dan-Isa da Kagara da ke ciki karamar hukumar Kauran-Namoda.

A yayin gudanar da zanga-zangar, sun mamaye titunan birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara domin nuna fushinsu kan yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankunansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng