Jama'a Sun 'Dimauce da Tankokin Mai Su ka Fashe a Zariya
- Wata tankar mai ta fashe a unguwar Dan Magaji, Zariya, jihar Kaduna, lamarin da ya jawo jama'a su ka fara gudun neman tsira da rai
- Fashewar ta haifar da hayaki mai kauri da ya rika tashi sama, lamarin da ya hana jama'a da direbobi ganin gabansu yadda ya kamata
- Lamarin ya faru ne bayan tankokin mai biyu da motocin hawa kirar Golf su ma guda biyu su ka yi arangama a yankin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – An samu mummunar fashewar tankar mai a unguwar Dan Magaji, garin Zariya, da ke jihar Kaduna.
Lamarin da afku bayan tankar man da wata motoci kirar Golf ta yi taho mu gama, lamarin da ya jawo kara mai tsanani har sau biyar da ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tashin hankali.

Source: Facebook
Zagazola Makama, da ya wallafa faruwar lamarin a shafinsa na X ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar masa cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tanka ta fashe a garin Zariya
Shaidun gani da iso sun bayyana cewa wani hayaki mai kauri ya turnuke saman inda tankar ta ke, abin da ya sa jama’a suka rika gudu domin tsira da rayukansu.
Sun ce hayakin da ya rika tashi sama ya hana wasu direbobi da masu tafiya a ƙafa ganin gabansu yadda ya kamata.
Shaidun sun kara da bayyana cewa karar fashewar tankar ta yi nisan zango, domin ta kai unguwannin da ke nesa da unguwar Dan Magaji da lamarin ya afku.
Jami'ai sun kai dauki a Zariya
A cewar rahoton, dukkanin mutane biyu da ke cikin motoci kirar Golf sun rasu nan take, kuma ba a kai ga gano adadin wadanda su ka jikkata ba.

Kara karanta wannan
Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi

Source: Original
Hukumomin da lamarin ya rataya a wuyansu na ci gaba da tattara bayanai domin gano girman barnar da lamarin ya jawo.
Hukumomin tsaro sun shawarci direbobi da masu tafiya a ƙafa da su guji bi ta hanyar da abin ya shafa, domin bai dace a shiga yankin ba a halin yanzu.
Sun ce jami’an agajin gaggawa da na kashe gobara suna ci gaba da aiki tukuru wajen shawo kan lamarin da kuma kare yaduwar gobarar zuwa wasu wurare.
Dakarun ‘yan sanda, jami’an tsaro da kuma ma’aikatan hukumar kashe gobara sun isa wurin da gaggawa bayan faruwar lamarin, domin tabbatar da tsaro da kuma taimakawa wajen kashe gobarar da ta tashi.
Tankar mai ta fashe a Neja
A baya, kun samu labarin cewa Wata tankar mai ɗauke da man fetur ta kama da wuta a gidan man A.A Rano da ke Hannun Riga, kusa da babban asibitin Kontagora, a jihar Neja.
Gidan man da lamarin ya auku yana nisan ‘yan mitoci kaɗan daga ofishin rundunar ‘yan sanda a Kontagora, kuma wutar ta tashi ne da yammacin ranar Lahadi, 23 ga watan Maris, 2025.
Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a tsaka da sauke mai a gidan, kuma babu wanda ya rasa ransa, yayin da mutane na cikin gidan man da waje su ka tsere domin tsira da rayukansu.
Asali: Legit.ng

