An Yi Rashi: Tsohon Sanata kuma 'Dan Amanar Buhari Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Rashi: Tsohon Sanata kuma 'Dan Amanar Buhari Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An yi rashi a jihar Neja bayan rasuwar daya daga cikin sanatocin da suka yi wakilci a majalisar dattawan Najeriya a shekarun baya
  • Sanata Ibrahim Musa wanda ya taba wakiltar Neja ta Arewa ya yi bankwana da duniya ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Agustan 2025
  • Marigayin wanda yake cikin 'yan amanar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rasu ne bayan ya yi 'yar gajeruwar rashin lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Tsohon Sanata mai wakiltar yankin Neja ta Arewa, Sanata Ibrahim Musa, ya yi bankwana da duniya.

Marigayi Sanata Ibrahim Musa ya je majalisar dattawa ne a ƙarƙashin jam’iyyar CPC, daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Sanata Ibrahim Musa ya yi bankwana da duniya
Sanata Ibrahim Musa ya rasu bayan ya yi jinya Hoto: Abubakar Musa
Source: Facebook

Jaridar Leaderahip ta rahoto cewa sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, ya tabbatar da rasuwar a cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ibrahim Musa ya rasu bayan jinya

Kara karanta wannan

APC ta yi wa Tinubu alkawari yayin da ta jaddada mubaya'a ga Ganduje a Kano

Alhaji Abubakar Usman ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Agustan 2025.

Ana yi wa marigayin kallon ɗaya daga cikin 'yan amanar tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari.

“Sanata Ibrahim ya rasu a yau (Alhamis) a birnin Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya bar mana tarihin sadaukarwa da jajircewa ga jama’arsa da ƙasa gaba ɗaya."

- Alhaji Abubakar Usman

Alhaji Abubakar Usman ya bayyana jimami mai girma a madadin gwamnatin jihar Neja da mutanen jihar dangane da rasuwar tsohon Sanatan.

'Dan majalisar Neja ya yi ta'aziyya

Dan majalisa daga jihar Neja, Abdullahi Idris Garba ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin.

A wani rubutu a shafinsa na Facebook, ya jajantawa iyalansa mutanen jihar Neja bisa wannan babban rashin da aka yi.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin al'ummarsa wanda yake da muradin ganin ci gaban mutanensa.

Sanata Ibrahim Musa ya rasu
Sanata Ibrahim Musa ya yi bankwana da duniya Hoto: Rep. Abdullahi Idris Garba - AIG
Source: Facebook
“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Ina miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokansa da kuma jam’iyyar APC ta jihar Neja, bisa rasuwar ɗan’uwanmu kuma babban ɗan majalisa, marigayi Sanata Ibrahim Musa."

Kara karanta wannan

Sanusi II ya rufe bakin mutane, ya je gidan Buhari domin yin ta'aziyya ga iyalansa

"Ina roƙon Allah ya gafarta masa zunubansa ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus."
"Sanata Ibrahim Musa, lauya ne a Najeriya, wanda ya zama Sanata mai wakiltar yankin Neja ta Arewa a zaɓen watan Afrilun 2011."
"Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin ɗan majalisa na gari, kuma mai kishin al’umma, wanda kullum yana da muradin ganin cigaban jama’ar da yake wakilta."
"Ina kuma roƙon Allah (SWT) Ya bai wa iyalan marigayin da abokansa haƙuri da juriyar wannan babban rashi."

- Abdullahi Idris Garba

Mahaifin 'Dan Bello ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mahaifin matashi dan gwagwarmaya, Bello Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello ya riga mu gidan gaskiya.

Ainihin takamaiman dalilin rasuwar marigayin ba su bayyana ba, amma wasu majiyoyi sun bayyana cewa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.

Daya daga cikin abokan Dan Bello, lauya Abba Hikima, ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifin na abokinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel