Ana Zargin an Yi wa Sowore Mummunan Rauni a Wajen 'Yan Sanda

Ana Zargin an Yi wa Sowore Mummunan Rauni a Wajen 'Yan Sanda

  • Ana zargin jami’an ‘yan sanda sun yi ƙoƙarin jawo Omoyele Sowore da karfi, inda ya samu wani mummunan rauni a hannunsa
  • Amnesty International na kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin Sowore ba tare da wani sharadi ba, tare da dakatar da cigaba da tsare shi
  • Tun 2019 ake tsare da Sowore bisa zarge-zarge daban daban, wanda Amnesty ta ce hakan na nuna yunkurin danne masu sukar gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya, Amnesty International, ta bayyana damuwa matuƙa dangane da tsare ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore.

Kungiyar ta ce an yi wa Sowore rauni hannu yayin da aka yi kokarin fito da shi daga wajen da ake tsare da shi.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kara kamen dilan kwaya a Kano bayan gagarumin samame

Amnesty ta bukaci a saki Sowore da gaggawa
Amnesty ta bukaci a saki Sowore da gaggawa. Hoto: Omoyele Sowore
Asali: Twitter

Amnesty ta wallafa a X cewa lamarin ya faru ne a yau Alhamis da misalin karfe 6:00 na safe, kuma daga bisani an tafi da shi wani wuri da ba a bayyana ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin tauye haƙƙin ɗan adam da kuma bijirewa dokar kasa da ke tanadar da bin matakan doka da oda.

Tsare Sowore: Kiran Amnesty ga hukumomi

A cikin wata sanarwa da Amnesty International ta fitar, ta bukaci hukumomin Najeriya da su dakatar da ‘yan sanda daga ci gaba da tsare Sowore.

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar ta kuma nemi a ba shi kulawar lafiya ta gaggawa saboda raunin da ya samu.

"An yi ƙoƙarin jawo shi zuwa kotu ba tare da kasancewar lauyansa ba, hakan abu ne da ya nuna take dokar kasa,”

- In ji sanarwar

Amnesty ta bayyana cewa gwamnati na da nauyin tabbatar da bin matakan shari’a da mutunta doka da oda a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Yadda Remi Tinubu ta raba tallafin N4.15bn a Najeriya a cikin shekara 1

Abin da ya faru da Sowore a baya

Kungiyar ta bayyana cewa tun shekarar 2019, an sha tsare Sowore ba tare da izini ba, tare da ƙaddamar da ƙananan shari’u da ke nuna rashin gaskiya.

A cewar Amnesty, a watan Nuwamba 2019 ne ta bayyana Omoyele Sowore a matsayin jarumi domin an sha tsare shi saboda ya fadi albarkacin bakinsa cikin lumana.

Sowore, wanda dan jarida ne kuma mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, ya fuskanci barazana daga jama'a da dama da gwamnati saboda ra’ayoyinsa masu zafi.

Dan gwagwarmaya Sowore a lokacin wata zanga zanga
Dan gwagwarmaya Sowore a lokacin wata zanga zanga. Hoto: Omoyele Sowore
Asali: Twitter

An bukaci ayi gaggawar sakin Sowore

Amnesty International ta bukaci a saki Sowore ba tare da wani sharadi ba tare da janye duk wasu zarge-zargen da ake masa.

Ta ce maimakon danne muryoyin masu sukar gwamnati, kamata ya yi gwamnati ta saurare su domin gyara matsalolin da ke damun al’umma.

Kungiyar ta kuma bukaci a bar Sowore ya ci gaba da amfani da haƙƙinsa na bayyana ra’ayi da gudanar da taro cikin lumana ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

Yadda Sowore ya jagoranci zanga zanga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya jagoranci zanga zanga a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa zanga zangar ta mayar da hankali ne kan halin da 'yan sanda suke ciki a Najeriya.

Sowore da wasu 'yan gwagwarmaya a Najeriya sun bayyana cewa sun yi zanga zangar ne domin kwatowa 'yan sanda da suka yi ritaya hakki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng