Bago: Kulle Gidan Rediyo da Sauran Lokutan da Gwamnan Neja Ya Jawo Cece Kuce

Bago: Kulle Gidan Rediyo da Sauran Lokutan da Gwamnan Neja Ya Jawo Cece Kuce

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya dauki wasu matakai da suka jawo cece-kuce kan mulkinsa.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wadannan matakai dai na Gwamna Bago suna jawo muhawara daga wajen mutane kan dacewarsu da akasin haka.

Gwamna Umaru Bago na jawo cece-kuce
Gwamna Umaru Bago ya umarci a kulle gidan rediyo Hoto: @HonBago
Source: Facebook

Mataki na baya-bayan nan da ya dauka shi ne umarnin rufe wani gidan rediyo.

Jaridar TheCable ta ce wannan ba shi ne karon farko da Gwamna Bago ke ɗaukar matakan da suka jawo cece-kuce tun bayan fara mulkinsa ba, musamman cikin watannin baya-bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu daga cikinsu nan kasa:

1. Rufe gidan rediyo

Lokacin da gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi 90.1 FM a ranar 31 ga Yulin 2025, hakan ya haifar da fushin jama’a da martani mai zafi.

Gidan rediyon, wanda ke Minna, babban birnin jihar, an zarge shi da watsa shirye-shiryen da ake zargin na ɗauke da ƙalubale da tayar da hankalin jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'

Bologi Ibrahim, sakataren yaɗa labarai na gwamnan, ya bayyana cewa “ayyukan yau da kullum na gidan rediyon sun saba ka’ida.”

Gwamna Bago ya kuma bayar da umarnin soke lasisin gidan rediyon, amma aka yi ta yi masa raddi.

2. Kalaman barazana a gaban Sarki

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya taba barazanar cafke duk wanda ya yi zanga-zangar adawa da matakin gwamnatinsa na kafa asibitin koyarwa na jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) a Minna, babban birnin jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta ce gwamnan yayin da kai ziyartar ta’aziyya ga Sarkin Lapai, Umaru Tafida, bisa rasuwar ɗan’uwansa, ya sha alwashin cewa zai hukunta duk wanda ya shiga zanga-zangar adawa da wannan mataki.

Gwamnan ya ƙara da cewa iyayen duk yaron da aka kama yana zanga-zanga suma za a cafke su kuma a kori danginsu daga garin Lapai.

"Na ji wasu ƙananan kwari na shirin yin zanga-zanga kan kafa IBBUTH a Minna. Allah ya basu ƙarfin gwiwar yin hakan."
"Amma idan suka kuskura, za su san ko waye Bago. Zan kulle su da iyayensu. Ko shakka babu kan hakan. Kuma bayan haka, zan kore su daga Lapai."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye

- Gwamna Umaru Bago

3. Cafke masu gashin dada

A watan Afrilun 2025, gwamnan ya bayar da umarnin kama matasan Minna da ke da gashin dada tare da umurtar a aske musu shi.

Tashar BBC Hausa ta ce gwamnan ya ce matakin yana ɗaya daga cikin kokarin da gwamnati ke yi don dakile laifuka da ɓarna, amma hakan ya haifar da suka sosai.

Gwamna Bago ya dage cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin tarbiyya ba.

“Duk wanda ku ka gani da gashin dada, ku kama shi, ku aske masa gashi, sannan ku sa masa tara"
“Ba wanda zai rika kowane irin aski a cikin Minna. Na ba jami’an tsaro umarni kan hakan."

- Gwamna Umaru Bago

Sai dai daga baya ya janye wannan umarni bayan fuskantar suka daga bangarori da dama.

Daga baya, Bago ya shaida wa masu zuba jari cewa suna da ’yancin zuwa jihar Neja “ko da suna da gashin dada”.

Kara karanta wannan

Ana jiran Tinubu ya karrama daliban Yobe, lauya ya gwangwaje su da kyaututtuka

4. Umartar marin malami

A watan Yuli, wani bidiyo da shafin Nigerianlawyer ya sanya a Facebook, ya nuna Gwamna Bago yana umurtar jami’an tsaro da su “mari” wani malamin addini a Minna.

Gwamnan ya ba da umarnin ne lokacin da ake gudanar da addu’o’i a gidan mataimakin gwamnan jihar kan rasuwar uwargidansa, Zainab Yakubu Garba.

Wannan lamari ya jawo fushin shugabannin addini da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, waɗanda suka zargi gwamnan da tauye haƙƙin faɗar albarkacin baki da ƙasƙantar da malamai.

Daga baya gwamnatin Neja ta bayyana cewa an fassara kalaman gwamnan ne ba daidai ba, amma hakan bai hana ci gaba da martani daga jama’a ba.

Gwamna Umaru Bago na shan suka
Gwamna Bago ya taba sanyawa a mari wani Hoto: @HonBago
Source: Twitter

5. Afuwa ga masu hukuncin kisa

A watan Yunin 2025, Bago ya sake shiga cikin cece-kuce bayan da ya yi afuwa ga mutane 11 da aka yanke wa hukuncin kisa, cewar rahoton jaridar The Punch.

Wannan matakin ya tayar da hankula a garin Gaba, inda matasa suka fito zanga-zanga, suna zargin gwamnan da buɗe ƙofa ga sababbin kashe-kashe da rikice-rikice.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gini ya rufta kan uwa da ƴaƴanta 5 a Katsina bayan mamakon ruwa

Iyalan waɗanda lamarin ya shafa, lauyoyi, da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun soki wannan mataki, suna mai cewa rashin hikima ne kuma babban koma baya ga adalci a jihar da ke fama da rashin tsaro.

6. Nada 'yan APC a hukumar zabe

A farkon watan Fabrairun 2025, Gwamna Bago ya naɗa Jibrin Imam, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar, a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Neja (NSIEC).

Jam’iyyar PDP ta yi ƙorafi kan wannan naɗi, tana cewa sauran waɗanda aka naɗa a hukumar NSIEC mambobi ne na jam’iyyar APC.

An maka gwamnatin Neja a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban karamar hukumar Chanchaga ya shigar da kara kan gwamnatin Neja a gaban kotu.

Alhaji Aminu Yakubu-Ladan ya shigar da karar kan matakin da gwamnatin ta dauka na rage wa'adin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli.

Daga cikin bukatun da ya nema a gaban kotun akwai dakatar da hukumar zaben jihar, gudanar da zabukan shugabannin kananan hukumomi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng