'Yan Kasar Waje Sun Yi wa Tinubu 'Wulakanci,' Firaminista Ya ba da Hakuri

'Yan Kasar Waje Sun Yi wa Tinubu 'Wulakanci,' Firaminista Ya ba da Hakuri

  • Firaministan St. Lucia, Philip Pierre ya ce sukar da wasu ke yi wa ziyarar Bola Tinubu ta ƙunshi wariyar kai da raina al’ummar Afirka
  • Philip Pierre ya ce sukar ta samo asali ne daga wasu ƙungiyoyi masu ɗauke da manufofin siyasa da goyon bayan jam’iyyar adawa
  • Pierre ya tabbatar da an cimma yarjejeniyoyi da Najeriya kan ilimi, yawon buɗe ido, lafiya da kasuwanci domin kara hada kan kasashen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saint Lucia – Firayim Ministan ƙasar Saint Lucia, Philip J. Pierre, ya caccaki masu sukar ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya kai ƙasarsu.

Ya yi magana ne yana mai cewa sukar ta nuna rainin hankali da nuna wariya da ke fitowa daga wasu 'yan adawa.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

Lokacin da Tinubu ke gaisawa da shugabannin St. Lucia
Lokacin da Tinubu ke gaisawa da shugabannin St. Lucia. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

NTA ta wallafa a X cewa Pierre ya yi wannan jawabi ne a ranar 1 ga watan Agusta, 2025, yayin bikin ranar 'yancin kasar a birnin Castries.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa sukar da wasu ke yi kan ziyarar Bola Tinubu wata alama ce ta baragurbin tunani da tasirin nuna wariya.

Ziyarar Bola Tinubu St. Lucia da amfaninta

A kwanakin baya ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara ƙasar Saint Lucia domin kulla alakar diflomasiyya da ƙasashen gabashin Caribbean.

Firayim Minista Pierre ya ce ziyarar ta haifar da yarjejeniyoyi da dama tsakaninsu da Najeriya, musamman a fannonin ilimi, lafiya, yawon buɗe ido da kasuwanci.

Ya bayyana cewa wannan ziyarar dama ce ta haɓaka haɗin kai da ƙasashen Afirka, musamman ganin irin alakar tarihi da ke tsakaninsu.

'Yan adawa sun caccaki ziyarar Tinubu

Pierre ya nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin ‘yan adawa musamman daga jam’iyyar UWP ke amfani da wannan ziyara wajen cimma wasu manufofin siyasa.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

Rahoton Jamaica Observer ya nuna cewa Pierre ya ce:

“Wannan sukar abin kunya ne kuma abin tozarci ne. Ta samo asali daga wariyar kai da raini kuma hakan bai dace ba.”

Firayim Ministan ya jaddada cewa bai kamata a kalli shugabannin Afirka da ƙasashensu da raini ba, inda ya kira hakan da ragowar tasirin nuna wariya.

Rahoton Unitedpac ya nuna cewa ziyarar Tinubu zuwa kasar ta jawo gagarumin ce-ce-ku-ce musamman daga wajen 'yan adawa.

Lokacin da aka karrama Bola Tinubu a St. Lucia
Lokacin da aka karrama Bola Tinubu a St. Lucia. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

St. Lucia za ta hada kai da Najeriya

A karshe, Pierre ya tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa ga aiwatar da yarjejeniyar da suka rattaba hannu da Najeriya.

Ya ce za su ci gaba da inganta alaka da Najeriya da sauran ƙasashen Afirka domin amfanin al’ummominsu a nan gaba.

Firaministan ya kuma yi kira da a girmama juna da ƙarfafa haɗin kai tsakanin nahiyar Afirka da ƙasashen yankinsa.

An karrama shugaba Tinubu a St. Lucia

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa an karrama shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yayin ziyara ta musamman da ya kai a kasar Sait Lucia.

Legit Hausa ta gano cewa an ba shugaba Bola Tinubu wata lambar yabo ce mafi girma yayin wani taro na musamman da aka shirya.

Bayan girmama shi, shugaba Tinubu ya mika godiya ga kasar St. Lucia tare da jaddada cewa Najeriya za ta cigaba da hada kai da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng