Sojoji da Mafarauta Sun Hada Hannu, An Yi Fata Fata da 'Yan Ta'adda

Sojoji da Mafarauta Sun Hada Hannu, An Yi Fata Fata da 'Yan Ta'adda

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun kai samame a jihohin Borno da Adamawa, a yayin da suke kokarin fatattakar 'yan ta'adda daga yankin
  • An kama mutane da ake zargi da kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki, an kwace babura, man fetur da na'urorin sadarwa da suke amfani da su
  • Iyalan ‘yan ta’adda 10 sun miƙa wuya a Bama, yayin da dakaru suka kwato makamai da kayan hada bam a yayin da ake ci gaba da kai farmaki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Dakarun Operation hadin kai tare da haɗin guiwar ɓangaren sojojin sama da mafarauta sun ƙara ɗaukar matakan fatattakar ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Sun yi wannan gagarumin aiki ne a tsakanin ranakun 15 zuwa 22 ga watan Yuli, 2025, inda aka samu nasarori a sassan shiyyar daban-daban.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Sojoji sun kashe babban kwamandan Boko Haram da mayaka masu yawa

Sojojin Najeriya sun kai hari kan 'yan ta'adda
Sojoji da mafarauta sun fatattaki 'yan ta'adda a Arewa Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro da masu sa kai na ƙara taimaka wa wajen raba yankin da 'yan ta'adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakarun Sojoji sun tarwatsa ‘yan ta’adda

Nigerian Army ta wallafa a shafin X cewa dakarun sun lalata hanyoyin samun kayayyaki da hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda da dama a jihohin Adamawa da Borno.

Wannan ya taimaka an kama mutane bakwai da ake zargi da kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki, tare da kwace babura, kayan abinci, man fetur da na'urorin sadarwa.

Sojojin kasar nan sun yi nasara
Sojoji na aikin kakkabe 'yan ta'adda a Arewa Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Dakarun sun kuma kai samame da farautar kwanton-bauna a kananan hukumomin Gwoza, Kaga, Bama, Monguno da Konduga, inda suka hallaka wasu daga cikin ‘yan ta’adda tare da dakile wasu hare-haren da ake shirin kaiwa.

Sojoji sun kama makaman ‘yan ta’adda

Daga cikin wadanda aka kama har da wani mutum da ke ɗauke da na’urar Starlink ba bisa ka’ida ba, da wani da ke dauke da tarin miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun daƙile mugun shirin ƴan ta'adda, sun kashe mai ɗaukar bidiyo domin yaɗa ƙarya

An kuma kwato makamai, kayan hada bam (IED), da kayan sadarwa. Baya ga haka, iyalai goma na ‘yan ta’adda sun miƙa wuya ga jami’an tsaro a karamar hukumar Bama.

A ranar 22 ga watan Yuli 2025, jami’an tsaro sun tare wata babbar hanyar safarar kayan aiki da suka hada da na’urorin zamani da wasu kayayyaki da ake shirin kaiwa yankin Gamboru.

Babban hafsan sojin ƙasa ya yaba da ƙoƙari da jarumtar dakarun, tare da tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta dauki aniyar tabbatar da an kawar da ta'addanci daga Arewacin Najeriya.

An gwabza fada da 'yan ta'adda

A baya, mun wallafa cewa Sojojin haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma (OPFY) sun dakile wani hari da gungun ‘yan ta’adda ke shirin kaiwa a ƙaramar hukumar Rijau, jihar Neja.

A wata sanarwa da Kyaftin David Adewusi, kakakin OPFY ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun fito ne daga yankin Baban Doka na ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Sojojin sun tarr 'yan ta'addan, inda aka gwabza da su a kusa da ƙauyen Inana da ke cikin Rijau, sannan aka samu nasarar fatattakar su bayan an samu hallaka wasu daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.