Hakeem Baba Ahmed Ya Fadi Kuskuren Tinubu kan Batun Sauke Shettima

Hakeem Baba Ahmed Ya Fadi Kuskuren Tinubu kan Batun Sauke Shettima

  • Ana ci gaba da cece-kuce kan batun ajiye Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Hakeem Baba-Ahmed ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan gum da ya yi da bakinsa kan lamarin
  • Ya nuna cewa idan har babu wani shiri a ƙasa, ya kamata a ce shugaban ƙasan ya fito ya yi watsi da jita-jitar rabuwa da Shettima

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya sake suka kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hakeem Baba-Ahmed ya soki Shugaba Tinubu ne kan shirun da ya yi dangane jita-jitar da ke ta yawo cewa yana da niyyar ajiye mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027.

Hakeem Baba-Ahmed ya soki Shugaba Tinubu
Hakeem Baba-Ahmed ya nuna kuskuren Shugaba Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed
Source: Facebook

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today'.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su iya kayar da Tinubu a 2027,' Hakeem Baba Ahmed

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana jita-jitar yin waje da Kashim Shettima

Ko da yake saura kusan shekaru biyu kafin zaɓen shugaban kasa na gaba, hasashe da jita-jita na ci gaba da yaɗuwa cewa ana shirin sauya Shettima daga takarar.

A watan Yuni, yayin da jita-jitar ta yi ƙamari, mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ƙaryata hakan, yana mai cewa ba batun da ya kamata a ɗauka da muhimmanci ba ne.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu zai yanke hukunci kan wanda zai yi masa mataimaki ne kawai bayan samun tikitin takarar APC.

Me Hakeem Baba-Ahmed ya ce kan Tinubu?

Sai dai a yayin tattaunawar, Hakeem Baba-Ahmed ya ce da a ce wannan magana ba ta da tushe, da shugaban ƙasa da kansa ya fito ya yi bayani a fili don kawo ƙarshen jita-jitar.

“Ina matuƙar sha’awar sanin dalilin da ya sa ake yawan yaɗa labaran cewa za a sauke Shettima. Gaskiya dai, ina ganin cewa shugaban ƙasa ya taɓa yin wani abu a can baya."

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Shugaba Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama sabon shugaban APC

- Hakeem Baba-Ahmed

A cewarsa, da Tinubu ya fito da wata sanarwa mai ƙarfi da ke nuna cikakken goyon baya da amincewa ga mataimakinsa, hakan zai kawo ƙarshen wannan jita-jita.

"Idan duk waɗannan labaran cewa za a ajiye mataimakin shugaban ƙasa domin wani daban, wataƙila wani ɗan Arewa ne, ko Kirista, ko daga wani wuri daban, ba su da wani tushe ko makama kwata-kwata, abu guda ne kawai zai hana yaduwar su"
"Shugaban kasa da kansa ya fito a fili ya ce, ‘Ku dakatar da wannan shirmen. Ina da cikakken ƙwarin gwiwa kan mataimakina. Ina aiki da shi lafiya, ina farin ciki da shi, kuma ina son wannan maganar shirmen cewa zan sauke shi, yanzu ko nan gaba, ta tsaya.’"
"‘Zan yanke hukunci kan wanda zai zama abokin takarata a 2027 idan lokacin ya yi. Amma a halin yanzu muna da aiki a gabanmu.’ Amma bai faɗi hakan ba. Mutanensa ma ba su faɗi hakan ba.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An gano abin da ya hana Atiku shiga ADC bayan ya baro Jam'iyyar PDP

"Abin damuwa ne, bari na faɗi gaskiya, abin damuwa ne. Idan abin da na faɗa shi ne ra’ayin shugaban ƙasa, to da ya kamata ya faɗe shi. Idan ba zai faɗi da irin kalaman da na yi ba, to da ya samo wata hanya, amma ya kamata ya fito daga gare shi da kansa ya zama kai tsaye kuma ya zama a fili."

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem Baba-Ahmed ya caccaki Tinubu
Hakeem Baba Ahmed ya ragargaji Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

Amaechi ya sha alwashin doke Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam'iyyar ADC a yankin Kudu maso Kudu, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin kan Shugaba Bola Tinubu.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya shirya hana dakatar da tazarcen Mai girma Tinubu a zaɓen 2027.

Tsohon ministan sufurin ya kuma buƙaci mutane da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin yin rajista da jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng