Dangote Ya Fadi Babban Kalubalen da Ya Ke Fuskanta a Matatarsa

Dangote Ya Fadi Babban Kalubalen da Ya Ke Fuskanta a Matatarsa

  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi magana kan wasu abubuwan da suka shafi matatarsa
  • Hamshaƙin attajirin ya bayyana cewa ƴan kasuwar mai na ƙasashen waje, suna wahalar da shi a matatarsa
  • Dangote ya bayyana cewa ya yi tunanin samun ɗanyen mai ba zai yi masa wahala ba, amma sai bayan da matatarsa ta fara aiki ya gane ya yi kuskure

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hamshaƙin attajiri, Alhaji Aliko Dangote, ya yi magana kan ƙalubalen da matatarsa ke fuskanta.

Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya bayyana cewa matatar ta na shigo da kimanin gangar ɗanyen mai miliyan 10 daga Amurka da sauran ƙasashe a kowane wata.

Dangote ya yi magana kan matatarsa
Dangote ya ce yana fuskantar kalubale a matatarsa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta ce Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabin sa na musamman a taron 'West African Refined Products Pricing and Markets Development Conference' da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

A cewarsa, kamfanonin mai na ƙasashen waje (IOCs) sune suka fi wahalar da shi a tafiyarsa wajen ginawa da kuma fara aikin matatar man, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Wace matsala Dangote ya fara fuskanta?

Ya ce bayan kammala aikin ginin matatar, babbar matsalar da suka fara fuskanta ita ce samun ɗanyen man da za a tace.

“Lokacin da muka fara aikin, abin da aka ɗauka a matsayin mai sauƙi shi ne samar da ɗanyen mai, musamman ganin cewa Najeriya na samar da gangar mai miliyan 2 a rana. Amma sai muka gano cewa mun yi kuskure."

- Alhaji Aliko Dangote

Attajirin ya ce, maimakon su riƙa sayen ɗanyen mai kai tsaye daga masu samar da shi a Najeriya a farashi mai sauƙi, sai suka riƙa siya daga manyan ƴan kasuwa na duniya.

Ya bayyana cewa waɗannan ƴan kasuwan suna sayen ɗanyen mai daga Najeriya su kuma sayar musu da shi a farashi mai tsada.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina Dikko Radda ya yi bayani daga asibiti bayan haɗarin mota

"Tabbas, kamar yadda muke magana a yau, muna sayen kusan gangar mai miliyan 9 zuwa 10 a duk wata daga Amurka da sauran ƙasashe."

- Alhaji Aliko Dangote

Dangote ya samu fetur daga NNPCL

Dangote ya ƙara da cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya ba su ɗanyen mai daga lokacin da suka fara aiki har zuwa yanzu.

“Sun yi ƙoƙari sosai. Amma mun sha sosai da IOCs. IOCs sune waɗanda suka fi wahalar da mu a duk tafiyarmu."

- Alhaji Aliko Dangote

Dangote ya fadi kuskuren da ya yi a matatarsa
Dangote ya tabo batun samun ɗanyen fetur a matatarsa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Karanta wasu labaran kan Dangote

Dangote zai daina shigo da fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar mai ta Dangote na shirin daina shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Matatar ta Dangote wacce ke a Legas ta shirya dakatar da shigo da ɗanyen man ne daga nan zuwa watan Disamban 2025.

Mataimakin shugaban matatar, ya bayyana cewa za su riƙa dogara ne da ɗanyen mai wanda aka samar a gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng