'Yan Sanda Sun Bude Wuta kan Masu Zanga Zanga a Abuja

'Yan Sanda Sun Bude Wuta kan Masu Zanga Zanga a Abuja

  • An samu hargitsi a birnin Abuja yayin da ƴan sanda suka yi yunƙuri tarwatsa masu zanga-zangar adawa da rusau
  • Jami'an ƴan sanda sun buɗe wuta kan mutanen da suka fito zanga-zanga a ƙaramar hukumar AMAC
  • An dai buɗe musu wuta ne lokacin da suka yi ƙoƙarin shiga inda ake rushe musu gidajen na su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan sanda sun harbi wasu mutum biyu ƴan asalin babban birnin tarayya Abuja masu suna Sunday Danjuma da Jacob Audu.

Ƴan sandan sun harbi mutanen ne lokacin da suke ƙoƙarin tarwatsa zanga-zangar rushe gidaje a unguwar Karsana da ke cikin ƙaramar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC).

'Yan sanda sun yi harbi a Abuja
'Yan sanda sun harbi mutanen da suka fito zanga-zanga a Abuja Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Shugaban unguwar Karsana, Zakari Baba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun buɗe wuta a Abuja

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Zamfara, an samu asarar rayuka

Ƴa ce ƴan sanda sun buɗe wuta ne lokacin da mutanen da ake rushe gidajensu suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin yankin da ƙarfi.

Zakari Baba ya ce rigima ta fara ne kimanin ƙarfe 10:00 na safe lokacin da ƴan sanda da ke tsaro a ƙofar shiga unguwar suka hana mutane shiga domin fitar da kayayyakinsu.

Ya ce wasu daga cikin mutanen sun yi ƙoƙarin shiga ƙofar da ƙarfi, wanda hakan ya sa ƴan sandan suka bude musu wuta.

"Gaskiya, a yanzu da nake magana, mutane biyu daga cikin mazauna unguwar da suka samu raunin harbin bindiga suna samun kulawa a cibiyar lafiya ta Gwagwa."

- Zakari Baba

Kwamishinan hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a (PCC) mai wakiltar Abuja, Hon. Musa Dikko, ya tabbatar da faruwar lamarin.

An raunata mutane a Abuja

Ya ce mutane biyu daga mazauna Karsana sun samu raunukan harsashi bayan da ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa su.

Ya ce ya kai ziyara unguwar domin kwantar da tarzoma, inda ya bayyana cewa ya gayyaci ɗan kwangilar zuwa ofishin hukumar domin ya bayyana wanda ya ba da umarnin rushe gidajen.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Rikakken dan bindiga ya shiga hannu bayan shekara 11 ana nemansa

'Yan sanda sun harbi masu zanga-zanga a Abuja
'Yan sanda sun bude wuta kan masu zanga-zanga a Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original
“Tabbas, na jagoranci wasu daga cikin jami’ai na zuwa unguwar lokacin da na samu kira na gaggawa cewa an harbi wasu mutum biyu mazauna Karsana."
"Kuma a yanzu da nake magana, mun sami nasarar kwantar da tarzomar, tare da gayyatar ɗan kwangilar zuwa ofishinmu domin ya bayyana bisa umarnin wa ya aiwatar da rusau ɗin."

- Hon. Musa Dikko

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, SP Adeh Josephine, ba ta ɗauki kiran waya ko ba da amsar saƙon da aka aika mata kan wannan lamari ba.

Ƴan bindiga sun yi wa ƴan sanda kwanton ɓauna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi wa jam'ian ƴan sanda kwanton ɓauna a Katsina.

Ƴan bindigan sun yi wa ƴan sandan kwanton baunan ne bayan da suka je kai ɗauki bayan sun samu kiran gaggawa kan ɓarnar da miyagu suke yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an tafka barna

A yayin artabun da aka yi, ƴan bindigan sun lalata mota mai sulke wacce jami'an ƴan sandan suke amfani da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng