Dan Bello, Sowore Sun Fara Zanga Zangar 'Yan Sanda a Abuja da Jihohi 36
- Tsoffin jami’an ‘yan sanda na kasa sun isa Abuja domin gudanar da babbar zanga-zanga saboda tsarin kudin fansho
- Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, da wasu masu fafutuka na shirin yin zanga-zanga a birnin tarayya
- Rundunar ‘yan sanda ta zargi wasu da amfani da batun jin dadin jami’an da suka yi ritaya don cimma wata manufa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yau Litinin, 21 ga watan Yuli, 2025 za a yi zanga zangar 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja da jihohi 36.
Tsoffin jami’an ‘yan sanda daga sassa daban-daban na kasar nan da kuma masu fafutuka ne suka fara shirin gudanar da zanga-zanga don neman hakkokinsu na fansho da walwala.

Source: Facebook
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a 2023, Omoyele Sowore ya wallafa a X cewa za su yi zanga zangar ba gudu ba ja da baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Korafin tsofaffin 'yan sanda kan fansho
Daily Post ta wallafa cewa shugaban kungiyar tsofaffin jami’an ‘yan sanda, Mannir M. Lawal, ya bayyana cewa babu abinda zai hana su gudanar da zanga-zangar lumana da suka shirya a Abuja.
Ya ce ‘yan kungiyar sun iso daga jihohi 36 don nuna damuwar su:
“Mun gana da Kwamishinan ‘yan sandan FCT, mun shaida masa cewa zamu gudanar da zanga-zanga.
"Muna so ne kawai a cire mu daga tsarin da fansho da muke ciki. A dawo mana da kudin da muka tara gaba daya,”
Ya karyata rade-radin cewa zanga-zangar wani yunkuri ne na bata wa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun suna. Ya ce:
“Bamu san da zanga zangar Sowore ba, sai yau da safe muka ga bayanin shi a kafafen sada zumunta.”

Source: Facebook
Sowore zai jagoranci zanga zanga
Omoyele Sowore, Dan Bello da wasu masu fafutuka sun bayyana aniyarsu ta gudanar da zanga-zanga a Abuja domin matsa wa gwamnati lamba kan jin dadin jami’an ‘yan sanda.
Sun bayyana cewa gwamnati bata dauki halin da jami’an ke ciki da muhimmanci ba, alhali suna taka muhimmiyar rawa a fannin tsaro da zaman lafiya a kasa.
Rundunar ‘yan sanda ta fadi matsayinta
Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa, Muyiwa Adejobi, ya ce wasu mutane suna kokarin amfani da batun jin dadin jami’ansu don biyan wata bukata ta siyasa.
Ya bayyana cewa:
“Zamu ci gaba da mai da hankali kan abin da ke gaban mu, wato jin dadin tsofaffin jami’an da suka sadaukar da rayukansu wajen kare kasa.”
Sowore ba zai shiga hadakar ADC ba
A wani rahoton, kun ji cewa Omoyele Sowore da ya yi takara a zaben shugaban kasar 2023 ya yi magana kan hadakar 'yan adawa.
Sowore ya bayyana cewa ba zai shiga wata hadaka da aka shirya ba domin bai amince da sahihanci tafiyar ba.
A bayanin da ya yi, dan gwagwarmayar ya ce mutanen da suke maganar hadakar ne suka lalata Najeriya a shekarun baya.
Asali: Legit.ng

