Majalisar Dattawa Ta Amince da Kirkirar Sababbin Jihohi 12? An Ji Gaskiya
- An yaɗa wasu rahotanni masu cewa majalisar dattawa ta amince da ƙirƙirar sababbin jihohi guda 12
- Sanata Shehu Buba Umar ya fito ya ƙaryata waɗannan rahotannin da aka yi ta yaɗawa a kafafen sada zumunta
- Ya bayyana cewa har yanzu majalisar ba ta zauna ba domin amincewa da buƙatar da ake da ita ta ƙirƙirar jiha ko ƙaramar hukuma
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Shehu Buba Umar, ya yi magana kan amincewa da ƙirƙirar sababbin jihohi.
Sanata Shehu Umar Buba ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa majalisar dattawa ta amince da ƙirƙirar sababbin jihohi 12.

Source: Twitter
Shehu Umar Buba ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Bauchi, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ba ta amince da ƙirƙirar jihohi ba
Ya bayyana rahoton amincewa da ƙirƙirar sababbin jihohin a matsayin ƙarya mara tushe kuma ba gaskiya ba ce.
Sanata Buba ya ce majalisar dattawa ba ta yanke wani hukunci ba dangane da ƙirƙirar sababbin jihohi ko ƙananan hukumomi.
Ya bayyana cewa majalisar dattawa ta kafa kwamitoci na jihohi domin gudanar da sauraron ra'ayin jama'a kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999, inda aka gayyaci ƴan Najeriya su bayar da shawarwarinsu, ciki har da buƙatun ƙirƙirar sababbin jihohi da ƙananan hukumomi.
An gudanar da sauraron ra’ayin jama’a a faɗin shiyyoyi shida na ƙasa, amma kwamitocin ba su kammala ba ko gabatar da rahotonsu ga majalisar tarayya.
“Babu wani rahoto da aka gabatar wa majalisa. Ba mu zauna ba domin mu tattauna ko mu amince da ƙirƙirar wata jiha ko ƙaramar hukuma."
- Sanata Shehu Umar Buba
Sanatan ya buƙaci al’umma da su yi watsi da rahoton da ke yawo wanda aka yi ƙaryar majalisar dattawa ta riga ta amince da ƙirƙirar jihohi 12.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi martani ga Turkiyya kan zargin bullar sabuwar kungiyar yan ta'addan FETO

Source: Twitter
An yaɗa rahoton ƙirƙirar jihohi
Tun kafin fara sauraron ra’ayoyin jama’a, majalisar dattawa ta karɓi buƙatu fiye da 46 na neman ƙirƙirar sababbin jihohi, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihar Katagum daga Bauchi.
Sai dai cire sunan Katagum daga jerin jihohin da ake cewa an amince da su ya jawo ce-ce-ku-ce da ruɗani a tsakanin al’ummar jihar.
Rahoton da ke yawo ya yi zargin cewa majalisar dattawa ta amince da sababbin jihohi daga kowace daga cikin shiyyoyin shida na ƙasa.
Sanata Natasha ta sa lokacin komawa majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta sanya lokacin da za ta koma bakin aiki a majalisar dattawa.
Sanata Natasha ta bayyana cewa za ta koma kujerarta a majalisar dattawa bayan hukuncin da kotu ta yanke.
Ta bayyana cewa tuni ta riga ta sanar da mahukunta a majalisar game da shirinta na komasa kan kujerarta.
Asali: Legit.ng
