Zaman Makoki: Kwankwaso Ya Rufe Bakin Masu Magana da Ya Ziyarci Gidan Buhari

Zaman Makoki: Kwankwaso Ya Rufe Bakin Masu Magana da Ya Ziyarci Gidan Buhari

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sauka a Katsina don kai ziyarar ta’aziyya bisa rasuwar Muhammadu Buhari
  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya samu rakiyar mataimakin gwamnan Kano da Alhaji Buba Galadima zuwa fadar Sarkin Daura
  • Mai martaba Sarkin Daura ya yaba wa Kwankwaso bisa girmama shugaba Muhammadu Buhari da ya dade yana yi tun kafin rasuwarsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina, Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauka a filin jirgin saman Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ranar Asabar, 19 ga Yuli.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Katsina ne domin ziyarar ta’aziyya a Daura bisa rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kwankwaso a filin jirgin saman Umaru Musa Yar'adua a Katsina
Kwankwaso a filin jirgin saman Umaru Musa Yar'adua a Katsina. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa bidiyon da ke dauke da bayanin da jagoran NNPP ya yi a fadar sarkin Daura a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Dantata: Gwamna Abba ya fadi abin da ke ransa kan ziyarar Tinubu zuwa Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya tafi Daura ne tare da mataimakin gwamnan Kano da kuma abokin tafiyarsa na siyasa, Alhaji Buba Galadima.

Sun kai ziyarar ne domin jajantawa dangin Buhari da kuma al’ummar Daura gaba ɗaya bisa wannan babban rashi.

A cikin ziyarar, Kwankwaso ya bayyana ta’aziyyarsa da addu’o’i ga mamacin, yana fatan Allah ya gafarta masa,

Kwankwaso ya gana da Sarkin Daura

A lokacin da suka isa Daura, Sanata Rabiu Kwankwaso da tawagarsa sun ziyarci fadar Sarkin Daura domin gabatar da gaisuwar ta’aziyya ga masarautar.

Jigon NNPP ya bayyana cewa mutuwar Buhari babban gibi ne ga Najeriya, musamman al’ummar Arewa.

Kwankwaso ya bayyana cewa Buhari ya yi gwagwarmaya wajen ganin Najeriya ta ci gaba da zama kasa mai mutunci da daraja.

Yadda aka yi salla domin girmama Buhari a Gombe
Yadda aka yi salla domin girmama Buhari a Gombe. Hoto: Aminu Malam|Bashir Ahmad
Source: Facebook

Kwankwaso ya rufe bakin masu magana

Ziyarar Kwankwaso ta kawo karshen jita-jita da ke cewa bai damu da mutuwar Buhari ba, domin wasu na cewa bai samu damar halartar jana’izar da aka yi a ranar Lahadi da ta gabata ba.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

A lokacin ziyarar, Kwankwaso ya jagoranci addu’ar neman gafara ga marigayi Buhari, lamarin da ya rufe bakin masu shakku kan damuwar shi da mutuwar shugaban.

Sarkin Daura ya yaba da rawar Kwankwaso

A jawabinsa yayin tarbar tawagar Kwankwaso, Sarkin Daura ya yaba da irin karramawar da Sanata Kwankwaso ya dade yana nuna wa Muhammadu Buhari tun kafin rasuwarsa.

Ya ce madugun Kwankwasiyya mutum ne mai girmama shugabanni kuma ya cancanci a yaba masa.

Sarkin ya kuma yi fatan ganin karin hadin kai tsakanin shugabanni na Arewa domin ciyar da yankin gaba.

Sanata Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga Sarkin Daura bisa tarbar da aka masa kai tsaye tare da tawagar shi

Ana zargin siyasatar da rasuwar Buhari

A wani rahoton kun ji cewa an fara samun sabani tsakanin 'yan ADC da jam'iyyar APC kan rasuwar shugaba Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar ADC mai adawa ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da shigar da siyasa cikin rasuwar tsohon shugaban kasar.

Sai dai fadar shugaban kasa ta karyata zargin da cewa shugaba Bola Tinubu ya fi karfin siyasantar da mutuwa domin neman suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng