An Gano Dalilin Ganduje na Rashin Tarbar Tinubu a Kano
- Hankalin jama'a ya koma kan yadda Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai samu damar tarbar Shugaba Bola Tinubu a jihar Kano ba
- Sai dai tuni tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano Muhammad Garba ya fitar da bayanai a kan dalilan rashin ganin Ganduje
- Garba ya jaddada cewa Ganduje yana da kyakkyawar alaƙa da Tinubu, kuma murabus dinsa bai shafi haɗin kansu da jam’iyyar APC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – A yammacin Juma'a, 18 ga watan Yuli ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci jihar Kano domin ta'aziyyar Alhaji Aminu Dantata.
Daga cikin abubuwan da suka ja hankalin jama'a shi ne rashin ganin tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a yayin tarbar.

Source: Facebook
BBC ta wallafa cewa a bayanin da tsohon shugaban ma'aikata gwamnatin, Muhammad Garba ya yi bayani a kan dalilin rashin ganin Ganduje a taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Ganduje na rashin tarbar Tinubu
Solacebase ta wallafa cewa Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa an sanar da Dr. Ganduje game da ziyarar Tinubu don ta'aziyyar Alhaji Dantata.
Sai dai duk da ƙoƙarin da ya yi na sauya jadawalin tafiyarsa da dawo wa Kano a cikin gaggawa domin tarbar shugaban ya ci tura.
Ya kara da cewa:
“Dr. Ganduje ya yi duk mai yiwuwa domin ya daidaita shirin tafiyarsa, amma hakan bai yiwu ba."

Source: Facebook
Garba ya ƙara da cewa ko da yake Ganduje yana ƙasar waje, yana ci gaba da tuntuɓar shugabannin jam’iyya a matakin ƙasa da jiha.
Muhammad Garba: 'Ganduje na tare da APC'
Sanarwar ta ci gaba da cewa Ganduje yana tare da APC da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a kowane lokaci.
Ya ce ko gabanin wannan tafiya, tsohon shugaban ya gana da jiga-jigan jam'iyya da suka hada da; Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Sauran sun hada da shugaban APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas da sauransu domin tabbatar da shirin tarbar Shugaba Tinubu ya tafi yadda ya kamata.
Ya ce murabus din Ganduje daga shugabancin APC bai da alaƙa bai haifar da matsala tsakaninsa da Shugaba Tinubu ba.
Muhammad Garba ya kara da jaddada cewa dangantakarsu na siyasa da girmamawa juna na nan daram.
A kalamansa:
“APC a Kano na nan daram cikin haɗin kai da biyayya ga Shugaba Tinubu da ajandar ci gaban Najeriya."
Tinubu ya yi ta'aziyyar Damfara
A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka Kano a ranar 18 ga Yuli, 2025 domin ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata.
Tinubu ya isa filin jirgin Malam Aminu Kano da yamma, bayan kammala jana’izar Muhammadu Buhari a Daura, inda magoya bayan APC da jami'an gwamnati suka karbe shi.
A ganawar da ya yi lokacin ziyarar, Tinubu ya bayyana cewa marigayi Dantata ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakon talakawa da dukiyarsa fisabilillahi.
Asali: Legit.ng

