Dantata: Gwamna Abba Ya Fadi Abin da Ke Ransa kan Ziyarar Tinubu zuwa Kano

Dantata: Gwamna Abba Ya Fadi Abin da Ke Ransa kan Ziyarar Tinubu zuwa Kano

  • Gwamnan jihar Kano ya yaba da ziyarar ta'aziyya da mai girma Bola Ahmed Tinubu ya kai kan rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata
  • Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa kan yadda shugaban ƙasan ya samu lokaci ya zo Kano domin yin ta'aziyyar marigayin
  • A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya yi addu'ar samun rahama daga wajen Allah Maɗaukakin Sarki ga marigayin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan ziyarar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai a jihar.

Gwamna Abba ya bayyana godiya ga Shugaba Tinubu bisa ziyarar da ya kai Kano domin jajanta wa al’ummar jihar da iyalan marigayi dattijo kuma fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Tinubu
Gwamna Abba ya godewa Shugaba Tinubu Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Zaman Makoki: Kwankwaso ya rufe bakin masu magana da ya ziyarci gidan Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya yabawa Bola Tinubu

A cewar sanarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana ziyarar Shugaba Tinubu a matsayin alamar tausayawa da jagoranci na gaskiya, wanda ya kawo ƙarin kwanciyar hankali ga al’ummar Kano da iyalan marigayi Dantata a wannan lokaci na jimami.

Sanarwar ta ƙara da cewa, tura tawagar jami’an gwamnatin tarayya zuwa wajen jana’izar a Madina, Saudiyya, da kuma matakan diflomasiyyar da shugaban ƙasa ya ɗauka don tabbatar da gudanar da jana’izar cikin kwanciyar hankali da mutunci, abin yabo ne da al’ummar Kano za su ci gaba da yaba wa.

“Dukkanin tsarin gudanar da jana’izar an aiwatar da shi cikin ƙima da nagarta, saboda goyon bayan mai girma shugaban ƙasa."
"Zuwa da kanka nan Kano, duk da cunkoson aikinka, alama ce ta jagoranci, tausayi da girmamawa."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Babban ɗan marigayin, Alhaji Tajudeen Aminu Dantata, shi ma ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƙasa Tinubu bisa yadda ya ba su goyon baya a lokacin rayuwa da kuma bayan rasuwar mahaifin nasu.

Kara karanta wannan

An gano dalilin Ganduje na rashin tarbar Tinubu a Kano

Ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ta daɗe tsakanin shugaban ƙasa da marigayin, tare da tabbatar da kudirin iyalan wajen ci gaba da ginawa kan abubuwan da mahaifinsu ke yi, waɗanda suka haɗa da tawali’u, hidima ga jama’a da kyautatawa.

Shugaba Tinubu ya je ta'aziyyar Dantata
Gwamna Abba ya yabi Shugaba Tinubu Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Dantata

A nasa bangaren, shugaban ƙasa Tinubu yayin da yake karrama marigayi Dantata, ya bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya, tawali’u da hidima ga al’umma.

"Muna cikin babban rashi na. Allah ya ji ƙansa, muna roƙon Allah cikin rahamarsa mara iyaka Ya sanya shi a Aljannah Firdaus."

- Shugaba Tinubu

Gwamna Abba ya cika alƙawura a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan alƙawuran da ya ɗaukarwa mutane a lokacin yaƙin neman zaɓensa.

Gwamna Abba ya bayyana cewa a cikin shekara biyu ya cika kaso 85% cikin 100% cikin alƙawuran da ya ɗaukarwa nutanen jihar.

Ya bayyana cewa abin da ya rage masa shi ne kaso 15% wanda yake sa ran cimma wa a cikin shekara biyu da suka yi masa ragowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng