'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Katsina, an Tafka Barna
- Ƴan bindiga sun tafka ɓarna bayan da suka kai harin ta'addanci a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Miyagun sun sace dabbobi masu yawa tare da raunata wasu mutane a harin da suka kai ƙaramar hukumar Kafur
- Hakazalika sun lalata mota mai sulke ta ƴan sanda a yayin musayar wutan da suka yi bayan sun yi musu kwanton ɓauna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga da ke ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Unguwar Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Juma'a da safe, inda suka sace dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba, tare da jikkata wasu mazauna ƙauyen mutum biyu.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina
Bincike da aka gudanar ya nuna cewa maharan sun kai harin ne inda suka kutsa cikin ƙauyen suka kwashe dabbobin kiwo, sannan suka tsere ta ƙauyen Rereji da ke makwabtaka da su a ƙaramar hukumar Malumfashi.
A yayin harin, ƴan bindigan sun harbi wasu mazauna ƙauyen guda biyu waɗanda aka bayyana sunayensu da Sani Yau da Umar Shamsu.
Dukkaninsu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga, kuma aka garzaya da su babban asibitin Malumfashi domin samun kulawar gaggawa.
Rundunar ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun mayar da martani ga harin.
Sai dai da isar jami'an tsaro, ƴan bindigan sun shirya musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta.
Ƴan bindiga sun lalata motar ƴan sanda
A yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindigan, tayoyin gaba na motar ƴan sanda mai sulke sun lalace, haka zalika injin motar ya samu mummunan lahani, wanda ya sa motar ta kasa ci gaba da aiki.
Duk da hakan, jami’an tsaro sun ɗauki matakin gaggawa, inda suka ƙara ƙaimi wajen gudanar da sintiri a yankin da kuma kaddamar da farautar maharan domin kamo su.

Source: Original
Wannan hari dai ya sake jaddada yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar wasu yankunan jihar Katsina, lamarin da ke kara jefa al’umma cikin fargaba da rashin tabbas.
Jami’an tsaro na ci gaba da aiki kafada da kafada da al’ummar yankin domin dawo da zaman lafiya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki sun fuskanci hukunci.
Lamarin ba daɗi
Kabir Salisu wani mazaunin Katsina ya nuna damuwa kan hare-haren ƴan bikdiga a jihar.
Ya.shaidawa Legit Hausa cewa ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen ɗaukar matakin da ya dace.
"Ƴan bindigan nan karensu kawai suke ci babu babbaka. Ya kamata su tabbatar sa cewa an kare rayuka da dukiyoyin al'umma."
- Kabir Salisu
Ƴan bindiga sun kashe manoma
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe manoma a wani hari da suka kai a jihar Plateau.

Kara karanta wannan
Jagoran yan ta'adda ya shiga hannu, ya fara ambato abokan hulɗarsa bayan ya ji matsa
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙaramar hukumar Riyom inda suka kashe mutum 27 ciki har da maza da mata.
Shugaban ƙungiyar matasan Berom ta ƙasa, Solomon Dalyop ya zargi Fulani makiyaya da ke kai harin kan mutanen yankin Bindi-Jebbu da ke ƙauyen Tahoss na ƙaramar hukumar Riyom.
Asali: Legit.ng

