Mutanen Daura Sun Fadi yadda Buhari Ya Rayu a tsakaninsu bayan Sauka a Mulki

Mutanen Daura Sun Fadi yadda Buhari Ya Rayu a tsakaninsu bayan Sauka a Mulki

  • Ana shirin birne gawar Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, inda ya kwashe shekaru biyu bayan barin mulki
  • Masu aikin gida da makwabta sun bayyana yadda Buhari ke nuna tausayi da ƙauna ga mutane har da dababbobi
  • Ahmad Lawan da wasu manyan baki sun ziyarci Daura domin girmama tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Yayin da ake shirin gudanar da jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a yau Talata an samu bayanai kan yadda ya rayu da mutane a Daura.

Wasu daga cikin ‘yan uwansa, makwabta, da masu aikin gida sun bayyana yadda ya rayu cikin sauƙi, natsuwa da tausayi a gidansa bayan ya bar mulki a 2023.

Shugaba Buhari a cikin gonar shi a Daura
Shugaba Buhari a cikin gonar shi a Daura. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Jaridar Punch ta yi tattaki zuwa gidan Buhari na Daura domin tattaunawa da mutanen da suka masa aiki da makwabta.

Kara karanta wannan

Yadda aka dauko gawar Buhari a jirgi daga London zuwa Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya rasu ne a wani asibiti da ke London ranar Lahadi 13 ga Yuli 2025, yana da shekaru 82 a duniya kuma za a birne shi a gidansa da ke Daura da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Masu aikin gidansa sun bayyana yadda Buhari ya ke nuna ƙauna ga dabbobi kamar raguna, dawaki da kuma tsuntsaye, lamarin da ya sa rayuwarsa ta ƙarshe ta kasance cike da annashuwa.

Rayuwar Buhari da dabbobi a Daura

Masu aikin gidansa sun bayyana yadda Buhari ya ke nuna ƙauna ga dabbobi kamar raguna, dawaki da kuma tsuntsaye, lamarin da ya sa rayuwarsa ta ƙarshe ta kasance cike da annashuwa.

Wani ma’aikacin gida ya ce:

“Marigayin shugabanmu yana da ƙaunar dabbobi musamman kunkuru guda uku da suka kai shekaru 28 da 30 da wani tsuntsu.
“Ya kan yi ta kallonsu yana murmushi. Wannan yana ƙara nuna irin siffar tausayi da jinkai da yake da shi tun kafin mulki.”

Kara karanta wannan

Mamman Daura: Bayanai sun fara fito wa kan rasuwar Muhammadu Buhari

Dangantakar Buhari da ma’aikatansa

Ma'aikatan sun kuma bayyana cewa Muhammadu Buhari ya ci gaba da zama da su cikin farin ciki da jin daɗi bayan barin mulki a 2023.

Wani daga cikin ma’aikatan ya ce:

“Shugabanmu bai taɓa nuna cewa mu ma’aikata ne kawai ba. Ya zamo mana uba da aboki, kuma yana halartar shagulgulanmu.”
“Na tuna yadda ya zo gidan wani ma’aikaci da ya rasa ɗa, ya zauna har na tsawon awa biyar yana tausaya masa. Wannan babban abu ne da ba za a manta da shi ba.”
An yi wa Buhari addu’o’i a Daura

Bayan gudanar da sallah a wani masallaci da ke Daura, limamin ya jagoranci addu’o’i na neman gafara da rahama ga marigayin. Jama’a suka amsa da “Amin” cikin hawaye da alhini.

Daya daga cikin abokan Buhari tun suna yara, Suleiman Ammali, ya ce:

“Fuskata tana bayyana ciwon da zuciyata ke ciki. Allah ne kadai ya san halin da nake ciki a yanzu, Buhari mutum ne da bai taba almundahana ba.”

Kara karanta wannan

'Akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu': Bidiyon haɗuwar Buhari da Tinubu na ƙarshe

“Na rasa aboki kuma shugaba. Arewa da Najeriya za su yi kewarsa matuƙa.”
Buhari tare da Sarkin Morocco a shekarun baya
Buhari tare da Sarkin Morocco a shekarun baya. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Wata maƙwabciya, Hajiya Bilkisu Isah ta ce:

“Sauƙin halinsa da halayyarsa za su dade suna cikin ran mu. Yana taimakon talakawa musamman a lokacin Sallah.”

Ismaila Ibrahim ya ƙara da cewa:

“Tun muna yara muka saba da shi, bai taɓa barin mulki ya canja shi ba. Yana raba abinci, raguna da kuɗi ga masu buƙata a kowane lokaci.”

An dauko gawar Buhari zuwa Daura

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya dauko gawar Muhammadu Buhari daga London.

Ana sa ran Kashim Shettima da tawagar gwamnatin Najeriya za su isa jihar Katsina da gawar da misalin karfe 12:00 na rana.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai karbi gawar a filin jirgin saman Katsina kafin daga bisani a wuce da ita Daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng