Kwana Ya Kare: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Rasu a London

Kwana Ya Kare: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Rasu a London

  • Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a birnin London bayan fama da rashin lafiya
  • Rasuwar tasa ta faru ne yau, inda tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad ya tabbatar da hakan cikin damuwa da alhini
  • Ana sa ran nan gaba kadan za a sanar da lokacin masa janaiza da dawo da gawar shi nan Najeriya daga London

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Birtaniya – Tsohon shugaban kasa na Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rasu a yau Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 a birnin London na ƙasar Ingila.

Labarin rasuwar tasa ya girgiza al’ummar Najeriya da ma kasashen duniya, inda fadar shugaban kasa ta tabbatar da faruwar lamarin bayan makonni na rade-radin rashin lafiyarsa.

Shugaba Buhari ya rasu
Shugaba Buhari ya rasu. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Legit ta gano cewa, mai magana da yawun marigayi Muhammadu Buhari, Garba Shehu ne ya wallafa labarin a shafin shi na X.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Tinubu ya tura Shettima ya ɗauko gawar tsohon shugaban kasa a London

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari, wanda ya shugabanci Najeriya daga 2015 zuwa 2023, ya shafe kwanaki da dama yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba a London kafin rasuwar tasa.

Buhari ya yi fama da jinya a London

Rahotanni sun ce Buhari ya kamu da rashin lafiya kuma ya yi jinya a wani asibiti a London, lamarin da ya jawo damuwa ga ‘yan Najeriya.

Sai dai tsohon hadimin Buhari a fannin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar bai yi jinya a ICU ba.

A yayin da ya ke yi wa Buhari fatan samun sauki kafin rasuwar shi, Bashir Ahmad ya ce:

“Gaskiya ne cewa Buhari na jinya, amma ba kamar yadda ake yada labarin yana cikin matsanancin hali ba.
"Yana samun sauƙi sosai kuma muna fata zai warke da wuri.”

Shettima ya ziyarci Buhari kafin rasuwar shi

A makon da ya wuce mataimakin shugaban kasa, Shettima ya sauka a London da sassafe ranar Litinin kuma ya shafe sa'o'i tare da Buhari yana masa jaje da isar da sakon Tinubu.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi': Tsohon shugaban kasa Buhari ya rasu, ƴan Najeriya sun magantu

Legit Hausa ta wallafa cewa, bayan tattaunawa, Shettima ya hada Buhari da Tinubu a waya kafin ya tashi daga asibitin.

Haka kuma, an bayyana cewa Shettima ya kai ziyara ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda shima yana jinya a London a lokacin.

Ana cigaba da jimamin rasuwar Buhari

A yanzu haka dai fadar shugaban kasa ta tabbatar da rasuwar shugaba Muhammadu Buhari a birnin London.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan rasuwar shugaban da ya sauka kafin hawan shi mulki.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa an tura Kashim Shettima zuwa London domin dauko gawar Buhari.

Nan da wani lokaci ake sa ran za a samu cikakken bayani kan yadda za a yi wa Baba Buhari jana'iza a Najeriya.

Buhari ya ki karbar cin hanci a Villa

A wani rahoton, kun ji cewa mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi magana kan rayuwar da ya yi a Villa.

Kara karanta wannan

An jiyo abin da Tinubu ya faɗawa Garba Shehu game da Buhari bayan ya ci zaɓe

Garba Shehu ya bayyana cewa an yi kokarin ba shugaba Buhari cin hanci ta hanyoyi da dama amma ya ki karba.

Baya ga haka, Garba Shehu ya kara da cewa an ware wasu makudan kudi domin kara yawan kasafin kudin abincin fadar shugaban kasa amma Buhari ya ki yarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng