Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya bayan Makonni a Kasashen Waje
- Jirgin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ya ziyarci ƙasashe biyu
- Mai girma Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya ne bayan ya ziyarci ƙasashen Saint Lucia da Brazil domin halartar wasu tarurruka
- Shugaban ƙasan ya samu tarba daga wajen manyan jami'an gwamnati bayan ya sauka filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan tafiye-tafiyen da ya yi zuwa ƙasashen waje.
Shugaba Tinubu ya dawo gida ne bayan ziyarce-ziyarcen da ya kai zuwa ƙasashen Saint Lucia da Brazil.

Asali: Twitter
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin shugaban ƙasan ya sauka a filin jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Asabar (lokacin Najeriya), bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Galeão da misalin ƙarfe 12:50 na rana (lokacin ƙasar Brazil).

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta caccaki El Rufai, ta fadi abin da zai sa Tinubu ya yi tazarce
Tinubu ya ziyarci Saint Lucia da Brazil
A ranar 28 ga watan Yuni, Shugaba Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa ƙasashen Saint Lucia da Brazil domin ziyartar ƙasashen biyu.
Wuri na farko da Shugaba Tinubu ya tsaya shi ne a Saint Lucia, inda ya kai ziyara a wani ɓangare na ƙoƙarinsa na zurfafa dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen Caribbean da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Kudancin duniya.
A lokacin ziyararsa a Saint Lucia, Shugaba Tinubu ya kai gaisuwar ban girma ga Gwamna-Janar na ƙasar, Mai Girma Cyril Errol Melchiades Charles, da Firaminista Philip Pierre.
Wani muhimmin ɓangare na ziyarar shi ne jawabin da Shugaba Tinubu ya gabatar a gaban zaman haɗin gwiwar majalisar dattawa da ta wakilai ta Saint Lucia da aka gudanar a William Jefferson Clinton Ballroom, Sandals Grande, Gros Islet.
A wannan zaman an samu halartar shugabannin ƙasashen ƙungiyar OECS manyan jami’an gwamnati, jakadu, ƴan Najeriya mazauna ƙasar, da darakta janar na OECS, Dr Didacus Jules.
Daga Saint Lucia, Shugaba Tinubu ya wuce ƙasar Brazil domin halartar taron ƙolin BRICS karo na 17 a birnin Rio de Janeiro.
Shugaba Tinubu ya samu gayyata daga shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, domin halartar taron, la’akari da matsayin Najeriya a matsayin “ƙasa abokiyar hulɗa”, wato ba cikakkiyar mamba ba, amma mai kusanci da ƙungiyar.
Shugaban ƙasan ya kasance a Saint Lucia daga ranar 29 ga Yuni zuwa 4 ga Yuli a yayin ziyarar tasa.
Daga nan sai ya wuce Brazil domin halartar taron ƙungiyar kasashe masu tasowa na Kudancin Duniya daga ranar Asabar, 5 ga Yuli zuwa Litinin, 7 ga Yuli.
Shugaba Tinubu ya samu tarba a Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu tarba daga wajen manyan jami'an gwamnati bayan ya dawo gida Najeriya.
Daga cikin waɗanda suka tarbi Shugaba Tinubu akwai ministan tsare-tsare da kasafin kuɗi, Alhaji Abubakar Atiku, Alhaji Ibrahim Masari, Sanata Aliyu Wamakko, ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, da mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan
2027: Malamin addini ya ja kunnen Tinubu, ya fadi abin da zai kawo masa cikas kan tazarce
Hadimin Tinubu ya caccaki El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya caccaki Nasir El-Rufai.
Sunday Dare ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna bai da wani tasirin da zai yi a lokacin zaɓe.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai yi tazarce a zaɓen 2027 saboda manufofin da gwamnatinsa ta aiwatar.
Asali: Legit.ng