'Yadda Buhari Ya Ki Karbar Sababbin Motocin N400m a Villa', Garba Shehu

'Yadda Buhari Ya Ki Karbar Sababbin Motocin N400m a Villa', Garba Shehu

  • Garba Shehu ya yi magana kan wasu halaye na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a cikin littafin da ya rubuta
  • Tsohon mai taimakawa shugaban ƙasan ya ce Buhari ya ƙi yarda a siyo sababbin motocin da zai riƙa amfani da su
  • Ya nuna cewa tsohon shugaban ƙasan ya kuma ƙi yarda a ƙara kasafin kuɗin abinci na fadar Villa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Garba Shehu, tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa da wani ƙudurin kashe Naira miliyan 10.

Garba Shehu ya ce an so kashe kuɗaɗen ne domin kasafin kuɗin abinci na fadar shugaban ƙasa a lokacin mulkin Buhari.

Garba Shehu ya fadi wasu halayen Buhari
Garba Shehu ya yi magana kan wasu dabi'un Buhari Hoto: @GarShehu
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce Garba Shehu ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa mai sunan ‘According to the President: Lessons from a Presidential Spokesperson’s Experience’, wanda aka ƙaddamar a Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Garba Shehu ya fadi dan takarar da Buhari ya fi so a zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Littafin ya bayyana abubuwan da ya fuskanta tsawon shekaru takwas da ya yi yana aiki a ƙarƙashin Buhari, tare da kawo bayanai daga bayan fage dangane da yadda ake tafiyar da mulki a fadar shugaban ƙasa.

Buhari na cin abincin talakawa

A cewar Garba Shehu, jim kaɗan bayan da Buhari ya hau mulki a shekarar 2015, an sanar da shi cewa dole ne a ƙara kasafin kuɗin abinci na fadar shugaban ƙasa zuwa Naira miliyan 10, wanda ya haɗa da abincin shugaban ƙasa, mataimakinsa, gidan baƙi da kuma liyafar hukumomi.

"Da suka ce ana buƙatar Naira miliyan 10, sai ya yi ihu ya buƙaci a rage kuɗin. Ya ce, ‘Duba teburina, me nake ci? Nawa ne kuɗin hakan?’”

- Garba Shehu

Garba Shehu ya bayyana abincin Buhari a matsayin mai sauƙi kuma mai lafiya.

"Dangane da yadda yake rayuwa cikin sauƙi, mafi yawan abincin da Buhari ke ci a matsayin shugaban ƙasa abinci ne na talakawa, wadanda ake ci a ƙasa cikin al’umma: tuwo (na masara ko gero), koko, ƙosai, wake, alkama, kayan lambu da yawa, kaji da naman raguna. Yana cin abinci mai lafiya sosai."

Kara karanta wannan

Garba Shehu ya fadi halin da Buhari yake ciki bayan kwantar da shi a asibitin Landan

- Garba Shehu

Buhari ya ƙi karɓar sababbin motoci

Shehu ya ƙara da cewa bayan hawansa mulki a 2015, babban sakatare na fadar shugaban ƙasa a wancan lokaci, Nebolisa Emodi, ya sanar da Buhari cewa an saki Naira miliyan 400 domin sayen sabbin motoci biyar na Mercedes-Benz da aka keɓe musamman.

Garba Shehu ya yi magana kan Buhari
Garba Shehu ya ce Buhari na cin abinci mai lafiya Hoto: @GarShehu
Source: Twitter
"An shirya wannan sayayya ne a ƙarshen mulkin shugaba Jonathan."
"Amma Buhari ya tambaya, 'Me ya samu motocin da shugaban ƙasa da ya gabace ni ya bari? Su dai sun ishe ni'."

- Garba Shehu

Garba Shehu ya ce Buhari ya ƙi amincewa da wannan sayayya, kuma ya umarci Emodi da ya rage yawan kuɗin gudanar da aiki a fadar shugaban ƙasa tare da ƙarfafa tsare-tsaren sarrafa kuɗi na cikin gida, rahoton Punch ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa Buhari ya ci gaba da amfani da motocin da Jonathan ya bari har sai da ɗaya daga cikinsu ta lalace a hanya lokacin da yake kan hanyarsa zuwa filin jirgin sama, sannan ne kawai ya canja mota.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta zargi wasu ƴan siyasa da ƙoƙarin gwara Buhari da Tinubu

Garba Shehu ya faɗi ɗan takarar da Buhari ya fi so

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai magana da yawun bakin shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya taɓo batun ɗan takarar da Muhammadu Buhari ya fi so a zaɓen 2023.

Garba Shehu ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan bai da wani ɗan takara da ya fi kwanta masa a rai daga cikin masu neman kujerar a lokacin.

Ya nuna cewa duk wanda ya zo wajen Buhari da batun niyyar yin takara, yana yi masa fatan alheri

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng