Abin da Ya Faru bayan Jami'an Tsaro Sun Kama Ɗan Bello a Filin Jirgi a Kano

Abin da Ya Faru bayan Jami'an Tsaro Sun Kama Ɗan Bello a Filin Jirgi a Kano

  • A ɗazu ne aka samu labarin cewa wasu jami'an tsaro sun damƙe Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Ɗan Bello a Kano
  • Sai dai jim kaɗan bayan haka, jami'an tsaro waɗanda ake zaton daga Abuja aka turo su, sun saki Ɗan Bello ba tare da ɓata lokaci ba
  • Ɗan Bello dai ya yi ƙaurin suna a Najeriya musamman a Arewa saboda yadda yake bankaɗo almundahanar ƴan siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano sun nuna cewa jami'an tsaro sun cafke fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Ɗan Bello.

Dr. Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Ɗan Bello, wanda ya yi kauren suna wajen tona badaƙalar ƴan siyasa ya shiga hannu a yau Asabar, 12 ga watan Yuli, a Kano.

Kara karanta wannan

'A shirye na taho daman': Ɗan Bello ya faɗi abin da ya faru bayan cafke shi a Kano

Fitaccen ɗan gwagwarmaya, Bello Habib Galadanci.
Jami'an tsaro sun saki Ɗan Bello jim kaɗan bayan kama shi a Kano Hoto: Dan Bello
Source: Facebook

A wani rahoto da DW Hausa ta wallafa a Facebook, ya ce ana zargin jami'an tsaron da suka kama Ɗan Bello daga Abuja suka zo musamman domin damƙe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an taaro sun saki Ɗan Bello

Jim kaɗan bayan kama shi, Leadership ta tattaro cewa jami'an tsaron sun saki Ɗan Bello ba tare da ɓata lokaci ba.

Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoto, babu wani bayani kan dalilin kama Ɗan Bello da kuma sakinsa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Ku daurari ƙarin bayani....

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262