A Ƙarshe, Garba Shehu Ya Yi Magana kan Batun Sa Wa Buhari 'Guba' a AC Lokacin Mulkinsa
- Malam Garba Shehu ya bayyana cewa ba shi da masaniyar an sa wa Buhari wani abu a AC wanda ya kwantar da shi rashin lafiya
- Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ce an yaɗa maganganu da dama lokacin da Buhari ke jiya, amma ba gaskiya ba ne
- An dai yaɗa jita-jitar cewa wasu daga cikin ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ne suka sanya wa Buhari guba a na'urar sanyaya yanayi watau AC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya yi ƙarin haske kan raɗe-raɗin da ake yi cewa an sa wa Muhammadu Buhari guba a AC.
Garba Shehu ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi rashin lafiya mai tsanani lokacin da yake mulki, amma ba shi da masaniya kan sa masa guba a na'urar AC.

Source: Twitter
Tsohon hadimin Buharin ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na kafar Channels tv ranar Juma'a, 11 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka yaɗa jita-jitar ciwon Buhari
Idan baku manta ba, a lokacin da Buhari ke fama da jinya a birnin Landan na ƙasar Igila, an yi ta yaɗa jita-jita kan ciwon da ke damunsa.
Wasu da dama sun yi zargin cewa guba aka sa wa Shugaba Buhari a masuburbuɗar sanyi watau AC, wanda ya yi sanadiyyar kwanciyarsa rashin lafiya.
Bayan shekaru biyu da sauka daga mulki, tsohon kakakin Buhari, Malam Garba Shehu ya yi ƙarin haske kan batun sa wa Buhari guba a AC.
Shin dagaske an sa wa Buhari guba a AC?
Da aka tambaye shi kan ko me aka sa a AC wanda ya kwantar da Buhari, Garba Shehu ya ce ba shi da masaniyar an sa wani abu a AC tun a lokacin har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan
Garba Shehu ya fadi halin da Buhari yake ciki bayan kwantar da shi a asibitin Landan
"Gaskiya ba san komai ba a lokacin, ban san wani abu da aka sa a na'urar sanyaya yanayi ta AC wanda ya sanya Buhari ya kamu da rashin lafiya ba.
"Ban taba neman sanin wace cuta ke damun shugaban ƙasa ko abin da ya jawo masa rashin lafiya ba tun wancan lokacin har zuwa yanzu.
"Na taƙaice maka ban taɓa tambyarsa ba, amma ina so ku sani batu na rashin lafiya abu ne na kai da kai, ko ni da kai, idan ba mu da lafiya, muna barin halin da muke ciki a matsayin sirri."
- Malam Garba Shehu.

Source: Getty Images
Garba Shehu ya ƙara da cewa an yaɗa maganganu da dama lokacin da Buhari ke jinya, wasu ma sun ce ya mutu, amma duk ba gaskiya ba ne.
Garba Shehu ya faɗi halin da Buhari ke ciki
A wani rahoton, kun ji cewa Garba Shehu ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na fama da rashin lafiya mai tsakani.
Tsohon kakakin shugaban ƙasar ya ce tabbas Buhari na kwance yana jinya a Landan, amma rashin lafiyarsa ba ta yi tsanani ba kamar yadda ake yaɗawa.
Tuni dai Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, don ziyartar Buhari a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Litinin, 7 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng
