Dantata: Dangote Ya Karbi Tawagar Gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

Dantata: Dangote Ya Karbi Tawagar Gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawaga mai karfi zuwa wajen iyalan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata a Madina
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shirye shiryen yi wa marigayin jana'iza a masallacin Annabi SAW a birnin Madina na Saudiyya
  • Rahoto ya nuna cewa sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya jagoranci addu’o’i na musamman ga marigayi Aminu Dantata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da iyalan margayi Aminu Alhasan Dantata a birnin Madina na Saudiyya.

Gwamna ya ziyarci gidan marigayin ne tare da wata tawaga da ta hada da sarkin Kano na 16, mai martaba Muhammadu Sanusi II.

Abba Kabir da Umar Namdi a Madina suna jiran jana'izar Dantata
Abba Kabir da Umar Namdi a Madina suna jiran jana'izar Dantata. Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

A karo na 2, an ƙara ɗaga jana'izar fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dawakin Tofa ya jaddada cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin ne ranar Talata, 1 ga Yuli, 2025, a masallacin Annabi SAW da ke birnin Madina.

Sanarwar ta ce iyalan marigayin sun tabbatar da cewa za a yi sallar jana’izar bayan sallar la’asar, inda dubban ‘yan Najeriya za su halarta daga sassa daban-daban domin karrama marigayin.

'Yan Kano da Jigawa sun gana da iyalan Dantata

Abba Kabir Yusuf tare da takwaransa na jihar Jigawa, Umar Namadi, da tsohon gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, a cikin tawagar da ta gana da iyalan marigayin.

Sauran da ke cikin tawagar sun hada da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II; Sarkin Karaye, Dr. Muhammad Mahraz; da shugaban ƴan kasuwar Kano, Alhaji Sabiu Bako,

Bugu da kari, a cikin tawagar akwai wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa daga Arewacin Najeriya.

Aminu Dantata da ya rasu yana da shekara 94
Aminu Dantata da ya rasu yana da shekara 94. Hoto: Hassan Mohammed
Source: Twitter

Ziyarar ta nuna yadda mutanen Arewacin Najeriya ke girmama marigayin da ya kasance ginshiki a fannin kasuwanci da agajin al’umma a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yadda Dangote ya raka gawar Dantata daga Dubai zuwa Madina

Dangote ya karbi tawagar Kano da Jigawa

Fitaccen attajiri, Alhaji Aliko Dangote da kuma ɗan uwan marigayin, Alhaji Tajuddeen Dantata ne suka karbi tawagar a inda aka yi zaman gaisuwa da jimami.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da Gwamna Umar Namadi sun bayyana alhini da kaduwar su bisa rasuwar dan kasuwar tare da addu’ar Allah ya jikansa.

Sarki Sanusi ya jagoranci addu’o’i ta musamman

Masarautar Kano ta wallafa a X cewa Muhammadu Sanusi II ya jagoranci addu’ar musamman ga marigayin, inda ya roƙi Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da aljanna.

Zaman ya haɗa fitattun mutane daga ciki da wajen Najeriya, ya zama wani babban karramawa ga Alhaji Aminu Dantata da ya rayu cikin hidima da taimako ga jama’a.

An dai tabbatar da cewa za a birne shi ne a makabartar Baki'a da ke birnin Madina, kamar yadda ya yi wasiyya kafin rasuwarsa a Abu Dhabi ranar Asabar.

Dangote ya raka gawar Dantata zuwa Madina

Kara karanta wannan

An shirya gudanar da jana'izar Alhaji Aminu Dantata bayan la'asar a Madina

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya raka gawar marigayi Aminu Dantata daga Dubai zuwa Madina.

Binciken Legit ya gano cewa marigayi Alhaji Aminu Dantata ya kasance kawu ga Alhaji Aliko Dangote.

An hango Alhaji Aliko Dangote tare da wasu daga cikin iyalan marigayi Aminu Dantata da suka hada da Alhaji Sanusi Dantata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng