ADA: INEC Ta Yi Bayani kan Yiwa Jam'iyyu Rajista gabanin 2027
- Hukumar INEC ta ce babu ƙungiyar da ta nemi rajista don zama jam’iyya a hukumance, duk da rahotonnin yan adawa sun yunkuro
- Rahotanni a baya-bayan nan sun bayyana cewa jagororin adawa sun mika bukata ga Hukumar Zabe domin samar da jam'iyyarsu
- Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kai na INEC, Sam Olumekun ya ce ba takardun nuna sha'awar zama jam'iyya su ka karba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa, har yanzu babu wata ƙungiya da ta gabatar da buƙatar rajistar sabuwar jam’iyyar siyasa.
Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a na INEC, Sam Olumekun, ya bayyana cewa, hukumar ta karɓi wasiƙun nuna sha’awar zama jam'iyya ne kawai.

Kara karanta wannan
Ana shirin tarar wa Tinubu, INEC ta faɗi sababbin jam'iyyun da aka nemi rijista kafin 2027

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a cewarsa, duk da yawan wasiƙun da suka karɓa, babu ɗaya daga cikinsu da ta nemi rajista ta zama jam’iyyar siyasa a hukumance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
INEC ta yi magana kan rajistar jam'iyyu
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Olumekun ya ce duk wata ƙungiya da ke son ta zama jam’iyyar siyasa dole ne ta bi ƙa’idojin da doka da tsarin gudanarwar rajista suka shimfiɗa.
Ya ce:
“Dole su cika ƙa’idojin farko kafin su aike da wasiƙar nuna sha’awa.”
Bayanin INEC na zuwa ne bayan rahotannin da ke nuna cewa Shugabannin adawa a Najeriya na neman yi wa ADA rajista a matsayin jam’iyya kafin zaɓen 2027.
Ana son hukumar INEC ta yiwa ADA rajista
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ke jagorantar wannan haɗakar ƙungiyar adawa da ke son samar da sabuwar jam'iyya. Akin Ricketts, shugaban ADA na kasa, da Abdullahi Musa Elayo, babban sakatare na wucin gadi, ne suka sanya hannu kan wasikar da aka aika wa INEC domin neman rajista.

Source: Twitter
Ana hasashen za su yi rajistar jam'iyyar ne domin samun damar buga wa da jam'iyya mai mulki ta APC a zaben 2027 da ke ƙarato wa.
Tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa kwaskwarima ya bai wa INEC ikon rajistar jam’iyyu da kuma soke wadanda suke da rajista idan akwai bukatar hakan.
TNN na son yin rajista da INEC
A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar siyasa mai suna Team New Nigeria (TNN) ta bayyana aniyarta ta neman rajista a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Ƙungiyar ta ce tana shirin cika dukkanin ƙa’idoji da sharuddan da INEC ke buƙata kafin ta miƙa buƙatar rijista, domin samun sahalewar zama cikakkiyar jam'iyyar siyasa.
Wannan sabon bayani daga TNN na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin ƙungiyoyi na shirin shiga takara a babban zaɓen 2027 don fafatawa da jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng
