Hajjin Bana: Saudiyya Ta Kafa Dokoki kan Masu Ɗaukar Hoto, Nuna Bangaren Siyasa

Hajjin Bana: Saudiyya Ta Kafa Dokoki kan Masu Ɗaukar Hoto, Nuna Bangaren Siyasa

  • Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a Saudiyya ta hana daukar hoto da rera wakoki ko daga tutoci a wuraren ibada yayin aikin Hajji 2025
  • Ma'aikatar ta ce haramun ne yin hoto da waya ko kayan daukar hoto a Masallacin Harami, Madina, Mina, Arafat da kuma Muzdalifa
  • Gwamnatin kasar Saudiyya ta ce aikin Hajji lokaci ne na ibada da hadin kai, kuma za a hukunta duk wanda ya karya doka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makkah, Saudiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun kawo wasu dokoki domin daƙile yawan aikata ba daidai ba.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a Saudiyya ta fitar da umarni mai tsauri da ke haramta daukar hoto, rera wakoki, da daga tutoci a wuraren ibada yayin Hajjin 2025.

Saudiyya ta sa doka kan masu ɗaukar hoto
Saudiyya ta hana ɗaukar hotuna yayin aikin hajji. Hoto: Haramain.
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa da Kamfanin dillancin labarai ta NAN ya samu a yau Laraba 4 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

'Ni kaɗai zan yi': Sarki ya haramta layya saboda tsadar rayuwa, zai yi wa ƴan kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hajji: Illar daukar hotuna da mahajjata ke yi

Mafi yawan mahajjata musamman daga Najeriya sun yi kaurin suna wurin dauke-dauken hotuna da bidiyo yayin aikin hajji.

Malamai da dama a Najeriya na yawan korafi kan abin da ke faruwa inda suke jan hankalin mutane kan haka.

Wasu malamai na ganin hakan zai ɗauke hankalin mutum wurin mayar da hankali kan ibada zuwa riya.

An kafa sababbin dokoki a aikin hajji
Hukumomi a Saudiyya sun hana daukar hoto yayin aikin hajji. Hoto: Hajj Reporters.
Source: Facebook

Saudiyya ta kafa doka kan daukar hoto

Ma’aikatar ta jaddada cewa mahajjata ba su da izinin daukar hoto ko bidiyo da waya ko kayan aiki a Masallacin Harami, Madina da sauran wuraren Hajji.

Wuraren da hakan ya shafa sun hada da Mina, Arafat da Muzdalifah, kuma ma’aikatar ta ce hakan yana cikin matakin tabbatar da tsari da ladabi.

Ta kuma bayyana cewa daukar tutoci ko wata alamar siyasa, kabila ko kasa ya saba da dokokin hajji kuma hakan ba za a yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Wata mahajjaciya daga Najeriya ta sake rasuwa a asibitin Makkah

Rera taken siyasa ko gudanar da wasu ayyuka na hadin gwiwa da ke da alaka da siyasa ko bambancin addini ya sabawa aikin Hajji, cewar rahoton Hajj Reporters.

Jami'ai a Saudiyya sun shawarci mahajjata

Jami’an sun bayyana cewa irin wadannan ayyuka na iya dagula natsuwa da tsarkin Hajji tare da haddasa sabani tsakanin mahajjata daga kasashe daban-daban.

Ma’aikatar ta sake jaddada cewa Hajji lokaci ne na tsarkake kai, ibada, da hadin kai, don haka duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci hukunci.

An bukaci mahajjata da su kiyaye dokoki tare da baiwa hukumomi hadin kai domin gudanar da Hajji cikin lumana da nutsuwa da kuma ibada.

An hana maniyyata 260,000 sauke farali

Mun ba ku labarin cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana mutum 269,000 shiga Makka ba tare da izini ba, yayin da suke kokarin shiga kasar.

An hana maniyyatan da suka je kasar domin sauke farali a wannan shekara ta 2025 saboda shiga ba bisa ka'ida ba.

Hukumomin kasar sun ce wannan wani mataki ne na dakile yawan maniyyatan da ke kokarin aikin hajji ba bisa tsari ba inda aka ce sai wanda ke da shaidar aiki hajji za a bari ya sauke farali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.