Bayan kashe DPO, 'Yan Daba Sun Farmaki Ofishin Hukumar NSCDC a Kano
- Ƴan daba sun kai hari a wani ofishin hukumar tsaro ta NSCDC da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano
- An kai harin ne bayan zargin wani mai satar waya ya rasa ransa a hannun wanda ya yi ƙoƙarin sace masa salula
- Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar NSCDC ya bayyana harin da aka kai kan ofishin na su a matsayin abin takaici
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƴan daba sun farmaki wani ofishin hukumar tsaro ta NSCDC da ke Gwazaye, ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Harin ya biyo bayan mutuwar wani da ake zargin mai satar waya ne, wanda ya rasa ransa a lokacin da yake ƙoƙarin ƙwace waya daga hannun wani mazaunin yankin.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce jami’in hulɗa da jama’a na NSCDC reshen jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mai satar waya a Kano
Ya bayyana cewa mutumin da lamarin ya faru da shi ya garzaya ofishin NSCDC mafi kusa da wurin, domin kai rahoto bayan mutuwar mai satar wayar.
Sai dai, bayan waɗanda suka kawo ƙarar sun bar wurin, jami’in hulɗa da jama’an ya ce wasu ƴan daba sun kawo hari, suna zargin cewa jami’an hukumar sun haɗa kai da wasu wajen kashe ɗaya daga cikinsu.
Duk da haka, Ibrahim Idris Abdullahi ya bayyana cewa hukumar NSCDC ta musanta hannun jami’anta a cikin lamarin, yana mai cewa ba su da alaƙa da shi illa kawai an kawo musu rahoto ne.
Me NSCDC ta ce kan kai hari a ofishinta?
"A ranar Litinin, 2 ga watan Yuni, 2025 da misalin ƙarfe 8:00 na dare, wasu ƴan daba guda biyu ɗauke da wuƙaƙe sun yi yunƙurin satar waya a Gwazaye, ƙaramar hukumar Kumbotso."
"Ɗaya daga cikin ƴan daban ya afka wa wani mazaunin yankin da ke yin waya, domin ƙwace wayarsa da ƙarfi."
“'Yan daban sun kusanci mutumin, ɗaya daga cikinsu ya kama shi da kokowa yana ƙoƙarin ƙwace wayarsa da wuƙa a hannunsa."
"A cewar wani ɗan sa-kai wanda ya ga lamarin da idonsa, yayin da ɗan daban ke ƙoƙarin ƙwace wayar, sai mutumin ya fi ƙarfinsa inda a hakan aka cakawa ɗan daban (wanda yanzu ya rasu) wuƙa a wuyansa."
"Mutumin (wanda lamarin ya faru da shi) tare da wasu makwabtansa uku, bayan faruwar lamarin, sun garzaya ofishin NSCDC da ke Semegu, ƙaramar hukumar Kumbotso domin kai rahoto."
"Abin takaici ne cewa wasu da ke ɗauke da makamai masu haɗari sun haɗu suka kai hari ofishinmu a yankin, suna zargin cewa waɗanda ke da hannu a lamarin jami’anmu ne.”
“Domin kawar da duk wani shakku, babu wani jami’in NSCDC da ya shiga cikin wannan lamari."
"Abin da ya tabbata shi ne waɗanda abin ya faru da su sun zo ofishinmu da ke Semegu domin kai rahoton yunƙurin satar waya, amma sai aka kai musu hari tare da ma’aikatanmu da ke wurin."
- SC Ibrahim Idris Abdullahi

Source: Original
Ya bayyana cewa yanzu haka sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ƴan sandan jihar Kano na gudanar da bincike a kan lamarin.
Ƴan bindiga sun farmaki jami'an NSCDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai farmaki kan jami'an hukumar NSCDC a jihar Bayelsa.
Ƴan bindigan sun farmaki jami'an ne yayin da suke sintiri a ƙauyen Igbomotoru da ke ƙaramar hukumar Southern Ijaw.
Wani jami'in hukumar ya rasa ransa a yayin musayar wuta da suka yi da miyagun ƴan bindigan masu ɗauke da makamai.
Asali: Legit.ng


