Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Iyalan 'Yan Wasa 22 da Suka Rasu a Hatsarin Mota
- Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta bayar da tallafin kuɗi ga iyalan ƴan wasan da suka rasu a hatsarin mota
- Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya sanar da cewa za a ba kowanne daga cikin iyalansu N1m
- Ya kuma bayyana cewa gwamnatin za ta ci gaba da kula da lafiyar waɗanda suka jikkata a sakamakon hatsarin motar da ya ritsa da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da N1m ga kowane iyali daga cikin iyalan matasan ƴan wasa 22 da suka rasa rayukansu a hatsarin mota.
Ƴan wasan sun rasa rayukansu ne a wani mummunan hatsarin mota yayin dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka gudanar a Abeokuta, jihar Ogun.

Source: Twitter
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ne ya sanar da hakan a ranar Asabar, 31 ga watan Mayun 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.
Gwamnatin Kano ta yi ta'aziyyar rasuwar ƴan wasa
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa asibitin Nasarawa a Kano inda aka adana gawarwakin waɗanda suka rasu.
Mataimakin gwamnan wanda ya yi magana a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi da ya taɓa zuciya, ba kawai ga Kano ba, har da gaba ɗaya ƙasar nan.
"Yau rana ce mai cike da baƙin ciki ga mu a Kano da ma gaba ɗaya Najeriya. Waɗannan matasa na dawowa ne daga wani aikin ƙasa bayan sun wakilci jihar Kano cikin girmamawa."
"Wasu daga cikinsu ma sun dawo da lambobin zinare. Abin takaici, tafiyarsu ta yanke suna dab da dawowa gida."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Za a tallafawa iyalan ƴan wasan da suka rasu
Baya ga tallafin kuɗi, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kuma bayar da abinci da kayan tallafi don rage wa iyalan mutanen da abin ya shafa raɗaɗin rashin su da suka yi.
"Mun riga mun tantance mutum 20 daga cikin waɗanda suka rasu, yayin da iyalan mutum biyu suka ɗauki gawarsu zuwa gida."
"Gwamna ya ba da umarnin cewa gwamnatin jiha ta tsaya tsayin daka tare da waɗanda abin ya shafa, kuma a tabbatar da cewa waɗanda suka jikkata sun samu kulawar lafiya ta musamman."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo

Source: Twitter
Mataimakin Gwamnan ya kuma ziyarci asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, inda ake kula da ƴan wasa bakwai da suka jikkata.
Ya jinjina musu, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta tallafa musu har su murmure gaba ɗaya.
Gwamna Abba ta hannun mataimakinsa, ya umarci a saki kuɗin tallafi nan da nan domin taimaka wa iyalan mamatan da kuma waɗanda suka jikkata.
Gwamnatin Kano ta ayyana ranar hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar hutu don jimamin ƴan wasan da suka rasu sakamakon hatsarin mota.
Gwamnatin ta bayyana ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar huti don jimamin wannan babban rashin da aka yi.
Ta buƙaci al'ummar jihsr da su yi amfani da lokacin wajen sanya mamatan cikon adduo'insu.
Asali: Legit.ng

