Ana Batun Hadaka, El Rufai Ya Fadi Kuskuren da 'Yan Najeriya Ke Yi kan Shugabanni
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya nuna damuwa kan yadda al'amuran mulki suka taɓarɓare a Najeriya
- El-Rufai ya bayyana cewa Najeriya ta kauce daga kan hanya domin an bari shugabanci ya koma hannun ƴan bindigan birni
- Tsohon ministan na birnin tarayya Abuja ya nuna cewa ƴan Najeriya sun saba miƙa mulki ga shugabanni waɗanda ba su san menene shugabanci ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, ya nuna damuwa kan tsarin shugabanci na yanzu a Najeriya.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ƴan bindiga da ke zaune a birane ne suka mamaye mulki a ƙasar nan.

Source: Twitter
El-Rufai ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Asabar yayin bikin cikar tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, shekara 60, a duniya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen taron an shirya wata lakca mai take: 'Amfani da talauci a matsayin makami na ragargaza Najeriya.'
El-Rufai ya ce Najeriya na cikin matsala
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa Najeriya na cikin gagarumar matsala, wacce ba ta taɓa shiga irin ta ba tun shekarar 1914.
El-Rufai ya bayyana cewa duba da hakan ne ya sanya suka yi azamar kafa haɗaka don dawo da ƙasar nan kan hanya.
“Najeriya na cikin mafi girman matsala tun daga shekarar 1914, shi ya sa muka haɗa kai muna aiki tare da ƙoƙarin kafa haɗaka, domin dawo da ƙasar nan kan hanya, domin yanzu ta kauce hanya."
“Ta kai wannan mataki ne saboda mun bar ƴan bindiga, ba na daji ba, amma waɗanda ke zaune cikin birane da ake kira ƴan bindigan birni, sun mamaye shugabanci."
"Ina ganin matsalar da muke da ita, wadda na fahimta cewa tsohon gwamna Babangida ya taɓa magana a kai, ita ce muna miƙa shugabanci ga mutane marasa ƙwarewa."
"Yawancinsu ba su san abin da za su yi da mulki ba, kawai dai sun san yadda ake karɓar mulki ne, amma ba su san yadda za su yi amfani da shi ba."
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
El-Rufai ya ba ƴan Najeriya shawara
Tsohon gwamnan ya buƙaci ƴan Najeriya da su farka daga barcin da suke yi, domin su riƙa zaɓar shugabannin da suka dace.
Ya jaddada cewa dole ne ƴan Najeriya su farka su zaɓi shugabannin da ke da ƙwarewa, basira, iya aiki, da jajircewa domin ciyar da ƙasar nan gaba.
Kotu ta samu El-Rufai da laifi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna, ta samu Malam Nasir El-Rufai da wasu mutane da laifi a ƙarar da aka shigar da su a gabanta.
Kotun ta yanke hukuncin cewa El-Rufai tare da wasu mutane za su biya diyyar N900m saboda tsare dattawan Adara da aka yi ba bisa ƙa'ida.
Kotun ta yi hukuncin cewa tsare dattawan da aka yi a lokacin da El-Rufai ke gwamna ya saɓawa doka, kuma take haƙƙin ɗan Adam ne.
Asali: Legit.ng

