An Kama Wanda Ya Shiga har Gida Ya Yi wa Matar Aure Yankan Rago a Kano

An Kama Wanda Ya Shiga har Gida Ya Yi wa Matar Aure Yankan Rago a Kano

  • Ƴan sanda a Kano sun kama wani matashi mai suna Shu’aibu Abdulkadir bisa zargin kashe Rumaisa Haruna mai shekara 22 da haihuwa
  • Shu’aibu ya amsa laifin kashe matar ne ta hanyar shake mata wuya da dankwali sannan ya yi mata yankan rago a cikin gidanta
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya yaba da kama shi da kuma kiran jama’a da su kasance masu lura da bada rahoto ga hukuma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama mutum ɗaya da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa wata matar aure a unguwar Tsamiyar Duhuwa.

Rahotanni sun tabbatar wa Legit cewa lamarin ya faru ne a cikin garin Kano a ranar 6 ga Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

An hallaka DPO a Kano yayin da rikici ya barke tsakanin matasa da 'yan sanda

Kiyawa
An kama wanda ya kashe matar aure a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a X, an ce bincike mai zurfi ne ya taimaka wajen kama wanda ake zargin.

Wanda ake zargin, Shu’aibu Abdulkadir, mai shekara 35 daga unguwar Madatai, ya amsa cewa shi ne ya shiga gidan matar da daddare ya shake ta da dankwalinta sannan ya mata yankan rago.

Yadda aka kashe matar aure a Kano

Binciken ya nuna cewa Shu’aibu ya kutsa cikin gidan Rumaisa Haruna, mai shekaru 22 da haihuwa, wadda ke zaune a Tsamiyar Duhuwa a Farawa, ya shake ta.

Bayan ya shake ta zai fita sai ya ga tana motsi har a lokacin, daga nan kuma sai ya shiga madafinta ya ciro wuka ya yanka wuyanta.

Mijinta, Ibrahim Mohammed, ne ya iske gawar matarsa da raunin yanka a wuya, kuma da aka garzaya da ita asibiti an tabbatar da mutuwarta.

Kara karanta wannan

Kano: Fusatattun matasa sun cinnawa ofishin ƴan sanda wuta, an ji abin da ya faru

Rundunar ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike, inda yanzu haka yana hannun hukuma yana taimakawa da ƙarin bayani.

Wanda ya kashe matar aure na so a kashe shi

Shu’aibu ya bayyana cewa bai taɓa kashe mutum ba a rayuwarsa, kuma ba ya amfani da miyagun ƙwayoyi. Ya ce yana zuwa makarantar Islamiyya da ta zamani, kuma yana koyon sana’ar dinki.

Ya ƙara da cewa ya yi nadama, kuma yana roƙon kotu ta yanke masa hukuncin kisa domin abin da ya aikata yana addabar zuciyarsa sosai.

Kwamishina ya yi kira da a haɗa kai a Kano

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da ƙoƙarin jami’an bincike da suka jajirce har suka cafke wanda ake zargin cikin gaggawa.

'Yan sanda
'Yan sanda sun nemi hadin kan jama'a a Kano. HotO; Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Ya kuma buƙaci jama’ar jihar da su ci gaba da lura da muhallinsu tare da bada rahoton duk wani abin da ya zama abin zargi domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Mutanen gari sun kashe DPO a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wasu matasa sun dauki doka a hannu wajen kai hari caji ofis a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a tsakanin matasa da yan sanda a Kano, ana fargabar an kashe DPO

Matasan sun kai hari wani caji ofis ne a karamar hukumar Rano ta jihar Kano inda suka afkawa wa jami'an tsaro.

Harin da matasan suka kai ya yi sanadiyar mutuwar shugaban 'yan sandan caji ofis din (DPO) da lalata dukiya mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng