Karfin Shugaban Rikon Rivers zai Ragu, Majalisa Ta Kafa Kwamitin Lura da Ayyukansa
- Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya kaddamar da kwamitin mutum 21 domin kula da harkokin dokoki a Jihar Rivers
- Kwamitin zai maye gurbin Majalisar Dokokin Rivers da aka dakatar bayan ayyana dokar ta-baci da Shugaba Bola Tinubu ya yi
- Majalisar tarayya ta bukaci 'yan kwamitin da su guji son rai tare da aiki da doka da gaskiya domin wanzar da zaman lafiya a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin wucin gadi mai mutum 21 domin kula da harkokin dokoki a Jihar Rivers.
Hakan na zuwa ne bayan ayyana dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sakamakon rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa an kaddamar da kwamitin ne a harabar majalisar a Abuja, inda Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas ya jagoranci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tajudeen Abbas ya ce matakin na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulki ya daura wa majalisar wajen tabbatar da doka da oda a fadin ƙasa.
Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye a majalisa, Farfesa Julius Ihonvbere, na da mambobi daga dukkanin shiyyoyi shida na kasar nan.
Rivers: Kwamitin majalisa zai fara aiki
Kakakin majalisar ya bayyana cewa kwamitin zai riƙa gudanar da harkokin majalisar dokoki a Rivers har sai an dawo da cikakkiyar dimokuraɗiyya a jihar.
Vanguard ta wallafa cewa Tajudeen Abbas ya ce:
“Ina kira da ku yi aiki da gaskiya, ku guji nuna son kai ko nuna bangare. Wannan aiki ne da zai tabbatar da ci gaban jihar da zaman lafiyar jama’ar ta,”
Ya ƙara da cewa dokar ta-bacin da Shugaba Tinubu ya ayyana a ranar 18 ga Maris, 2025 ta samu goyon bayan doka karkashin sashena 305 na kundin tsarin mulkin 1999.
Bukatar zaman lafiya a jihar Rivers
Abbas ya ce kwamitin ba wai kawai zai sa ido kan aikin mai rikon jihar, l Ibok-Ete Ekwe Ibas, ba ne kawai, har ma zai tallafa wajen tabbatar da sulhu da haɗin kai a Rivers.
Tajudeen Abbas ya yi wa kwamitin gargadi da cewa:
“Wajibi ne ku guji tsoma baki a siyasa kuma ku tabbatar da cewa kowane mataki da za ku ɗauka ya yi daidai da tsarin mulki,”

Asali: Facebook
Kwamiti ya ce zai yi gaskiya a Rivers
Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere, ya bayyana cewa wannan shi ne mafi ƙarfin kwamitin wucin gadi da aka kafa tun daga 2019, yana mai alƙawarin za su gudanar da aikinsu da gaskiya.
A karshe, kwamitin ya sha alwashin cewa zai yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomi domin dawo da doka da oda a Jihar Rivers.
Tompolo ya ce Fubara zai dawo mulki

Kara karanta wannan
Tsohon dan majalisa ya dauki matakin kotu da Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Ribas
A wani rahoton, kun ji cewa abokin ministan Abuja da aka fi sani da Tompolo ya ce yana kokari wajen sasanta rikicin Rivers.
Tompolo ya ce bisa kokarin da yake yi, yana da tabbas cewa nan gaba kadan gwamna Simi Fubara zai dawo kan karagar mulki.
Baya ga haka, Tompolo ya yi kira ga al'ummar Neja Delta su hada kai kuma su nisanci duk wani abu da zai kawo rashin tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng